Gwamnatin Jihar Kano ta hannun hukumar kula da zirga-zirga ababen hawa ta jiha KAROTA ta haramta wa matuka baburan adaidaita sahu bin manyan titunan tun daga ranar 30 ga watan Nuwambar 2022.
Gwamnatin ta dauki matakin ne bayan da ta samar da manyan motocin da za su dinga daukar al’umma a titinan da aka haramta wa ‘yan adaidaita sahun bi.
- Shugaban Rikon Kwarya Na Chadi Na Son Zurfafa Hadin Gwiwa Tare Da Sin
- Shugaban Rikon Kwarya Na Chadi Na Son Zurfafa Hadin Gwiwa Tare Da Sin
Sanarwar ta bayyana cewa an haramta wa direbobin baburan adaidaita sahun bin titinan Amadu Bello da Mundubawa zuwa Gazawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta tanadi manyan motocin sufuri domin saukaka wa al’umma bin wadannan hanyoyi.
Gwamnatin ta kara da cewa za ta sanar da ranar da matuka adaidaita sahun za su daina bin wasu manyan titinan da zarar gwamnatin ta samar da ababen hawan da a’lumma za su yi amfani da su a wadannan hanyoyi.
Kamar yadda jami’in yada labaran ofishin KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Nai’sa ya shaida wa Jaridar Leadership Hausa.