Hukumar asusun raya noma ta kasa da kasa ta Majalisar Dinkin Duniya (IFAD) ta bayyana cewa, ta bayar da daukin sama da Naira biliyan 16 a karkashin shirin bunkasa noma don samun riba (BCDP) a Jihar Beniwe.
Ta ce ta bayar da wannan daukin ne daga tsakanin 2016 zuwa 2024, ta hanyar yin amfani da kungiyar samar da kaya, wato CAF.
- Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
- Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka
Jami’ar shirin na IFAD-BCDP da ke garin Makurdi, Dakta Fatima Aliyu, ta bayyana hakan ne a wani taro na tsarin bayar da daukin BCDP.
A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar.
Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar.
Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin kai wajen shiga cikin tsarin na CAF, musamman a bangaren noman shinkafa da rogo da sauran amfanin gona.
Kazalika, ta bukaci mahukunta a jihar da su samar da tsari a hukumance, musamman na dogon zango domin ci gaba da samar da wadataccen abinci a fadin jihar baki-daya.
Shi ma a nasa bangaren, jami’in shirin na jihar; Dakta Emmanuel Igbaukum ya bayyana cewa, masu ruwa da tsaki a jihar, sun nuna sha’awarsu ta shiga cikin shirin tare kuma da sanya shi a cikin tsarin jihar na samar da abinci mai gina jiki.
Ya kara da cewa, shirin zai kuma taimaka matuka wajen kara bunkasa fannin aikin noma na jihar baki-daya.
A nata jawabin, Babbar Sakatariya a ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci, Pharm. Elijah ta bayar da tabbacin cewa; gwamnatin jihar za ta bayar da kason kudi a kan lokaci tare kuma da yin rangwame wajen sayen kayan aikin noma cikin rahusa.
Ta bayyana cewa, gudunmawar shirin na IFAD ya taimaka matuka wajen kara bunkasa fannin tattalin arziki da kuma fannin aikin noma na jihar.