Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta dakatar da yanke hukunci kan karar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku ya shigar na neman soke nasarar Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta bayyana cewa ta dakatar da yanke hukuncin ne saboda rashin makama tare da yin nazari a nan gaba.
- Kungiyoyin Magoya Bayan Kano Pillars Da Katsina United Sunyi Taro A Kano Domin Sulhunta Tsakanin Su
- Xi Ya Ba Da Umarnin Ceto Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Da Bala’o’in Yanayi Suka Rutsa Da Su
Yayin zaman kotun, Alkalin kotun, Mai Shari’a Simon Tsammani ya ce za a sanar da ranar da kotun za ta zantar da hukunci ga dukkan bangarorin guda biyu.
Atiku ya roki kotun da ta yi adalci ga karar da ya shigar, ba yanke hukuncin da zai iya zubar da kiman bangaren shari’a ba.
Ya dage kan cewa a soke nasarar Tinubu bisa la’akari da hukuncin da kotun Amurka ta yanke, inda ake zarginsa da safarar kudade ba bisa ka’ida ba da kuma ta’anmuli da miyagun kwayoyi.
Babban lauyan Atiku, Cif Chris Uche SAN ya gabatar da korafin a gaban kotu.
Sai dai kuma lauyan jam’iyyar, APC, Lateef Fagbemi SAN, ya bukaci kotun da ta yi watsi da hukunce-hukuncen da aka ce an yanke hukunci sama da shekara 30 da suka gabata.
A nasa bangaren, Shugaba Tinubu, wanda ya samu wakilcin babban lauya, Cif Wole Olanipekun SAN, ya yi nuni da cewa a yi watsi da karar saboda Atiku da PDP sun kasa gabatar da hujjar da zai sa a soke nasarar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bai wa Tinubu.