Kamfanin SINOMACH, zai kafa masana’antar sikari da kuma gonar rake da za su fara samar da tan 100,000 na sikari a duk shekara.
Hukumar Bunkasa Noman Rake ta Kasa (NSDC), ta sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan daya da kamfanin SINOMACH na Kasar Sin, domin habaka noman Rake da sarrafa shi a fadin wannan kasa.
- Bayan Shekaru 10 Madrid Da Barcelona Zasu Sake Yaɗuwa A Wasan Ƙarshe Na Copa Del Rey
- Yadda Cazar Kudade Da Yawa Ke Haifar Da Raguwar Fitar Da Kaya A Tashoshin Jiragen Ruwa – NPA
Ta yi hakan ne da nufin samar da wadataccen Sikari da yawansa ya kai kimanin tan miliyan daya.
Wannan dai, wani bangare ne na shirin kara habaka hada-hadar kawance tsakanin kasar da China.
Kazalika, hakan na daga cikin yunkurin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu, na jawo masu zuba jari da yawansa ya kai kimanin dala biliyan daya a fannin habaka samar da Sikari a kasar.
Bisa tsarin wannan yarjejeniya, kamfanin zai kafa masana’antar Sikari da kuma gonar Rake da za su fara samar da tan 100,000 na Sikari a duk shekara.
Kazalika, Hukumar NSDC ita kuma, za ta taimaka wajen samar da duk takardu da kuma sahalewar gwamnati da ake bukata, domin fara aikin.