Kwamishinan hukumar zaben Jihar Ribas, Obo Effanga ya bayyana cewa babban abin da ke rusa ci gaban kasar nan shi ne, yadda mafi yawancin ‘yan siyasan Nijeriya suke sayan kuri’u.
Ya ce hukumar zabe tana gudanar da wasu shirye-shirye masu karfi da zai tabbar dakile wannan mummunar dabi’a.
A kwanan nan ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tana nada Effanga a matsayin kwamishinan zaben Jihar Ribas. Ya bayyana hakan ne a lokacin wata liyafa da ta gudana a Abuja.
Ya ce, “A yanzu yadda ‘yan siyasa ke sayan kuri’u ya nuna cewa wadannan kuri’u suna da matukar muhimmanci kuma dole da su ne za su iya samun nasara a zabe. Saboda a yanzu ana kirga kuri’un mutane shi ya sa ‘yan siyasa suke bin duk wata hanya da za su sayi kuri’u,” in ji Effanga.
Ya kara da cewa ‘yan siyasa sun gano cewa watakila wannan ce hanya mafi saukin samun nasara shi ya sa suke bai wa mutane kudi domin su saye kuri’unsu.
Ya ce a bangaren INEC, duk mutumin da ya cancanci jefa kuri’a za a bar shi ya yi zabe. A cewarsa, lokacin da mutum ya yi zabe za a kirga kuri’arsa sa’ilin da aka kammala zabe.
Ya ci gaba da cewa dabi’ar sayan kuri’a tana matukar kawo matsala ga ci gaban kasa.
Kwamishinan zabe ya ce duk dan Nijeriya da yake da sha’awar samun dimokuradiyya mai inganci, ya tabbatar da cewa bai sayar da kuri’arsa ba. Ya ce hakan zai iya faruwa ne a lokacin da aka fadakar da ‘yan Nijeriya illar sayar da kuri’arsu.
Effanga ya ce gudanar da zabe a kan tsari shi ke karfafa dimokuradiyya, wannan shi ya sa manyan mutane a Nijeriya suka tashi tsaye na ganin cewa hukumar zabe ba ta samu cin gashin kanta ba, wannan ne ya sa mafi yawancin zaben kananan hukumomi ake tafka magudi na ganin sai jam’iyya mai mulki ta samu nasara.
Kwamishinan zabe ya bayyana cewa yin rajistar zabe fiye da daya ya janyo mafi yawancin mutane ba za su samu nasarar jefa kuri’a ba. Ya ce an dakatar da katin zabe na mafi yawancin mutane saboda sun yi rajista fiye da guda daya.