Wani kamfani mai zaman kansa da ke yin fashin baki kan haraji a kasar a kasar nan wato Tad Czar, ya bayyana cewa, mai yuwa, sauye-sauyen da Gwamantin Tarayya ta samar da bangaren haraji kasar za a tsame kaso uku na ma’aikatan kasar daga biyan harajin kudaden da suke samu.
A cewar Taiwo Oyedele, wanda ke jaorantar Kwamtin Fadar Shugaban Kasa a yanzu, kaso uku a cikin dari na ‘yan Nijeriya ne, ke samu Naira 100,000 a duk wata, wanda ya yi dai dai da dala 62 ko kasa da haka.
- Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
- Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232
Kwamtin ya dai shafe shekaru biyu, yana yin nazari kan harajin da kasar ke karbar
A cikin wani rahoto da kamfanin yin fashin baki kan tattalin arziki ya fitar ya snar da cewa, irin wadannan rukunin ma’aikatan, za a cire su daga sauye-sauyen biyan haraji.
Wannan sauye-sauyen na biyan harajin, an kirkiro da shi ne, bisa nufin gano asalin harajin da ake biya a kasar, wanda a yanzu kusan ya dogara kachokam kan kudaden da ake sau daga rarar sayar da Man Fetur.
Harajin ya kuma kai kasa da kimanin kaso 11 a cikin dari, wanda ya kai kasa da wanda ake karba, idan aka kwatanta da duniya.
“Abinda muka yi shi ne, mun cire daukacin ma’aikatan da karbar kasa kaso uku a cikin darei a cikin tsarin na karabar harajin,” Inji tsohon Shugaban LLP.
Ya shedawa manyan Malaman Makaranta da Jami’an da ke katbar haraji hakan ne, a wani taro da aka gudanar a jihar Legas
Nijeriya dai, ta kasance kasar da sama da alumominta miliyan 8o, ke fama da kangin talauci.
Hakan ya kuma kara haifar da hauhawan farashin kayan masarufi, musamman yadda kayan suka tashi a 2024, kafin su sauka zuwa kaso 24.2 a cikin dari.
Kazalika, hauhauwan farashi da sauye-sauyen da gwamnatin kasar ta kirkiro da su da cire tallafin Man Fetur da kuma faduwar darajar Naira, sun sanya kudaden shigar da ake samu a kaar, sun ragu.
An dai yiwa fasalin dokar karbar haraji kai da kai ne a kasar ne na karshe a 2011 a yayin da wasu ‘yan kasar, ke samun kudin shiga a duk shekara da suka kai Naira 3.6 a wancan lokacin.
Oyedele ya ci gaba da cewa, sai dai, a yanzu, an, na samun kudin shiga da suka kai kasa da Naira miliyan 1.7 a duk wata wanda suka kai daidai da dala 1,060.
Ana sa ran wannan Kwamtin, zai saita dokokin na karbar harajin, a zango na karashen na 2026.
Ana kuma sa ran, za daga kimar karbar harajin da ga wanda ake da shin a yanzu, na kaso 7.5 a cikin dari, zuwa kaso 10 a cikin dari, a 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp