Cigaba daga makon jiya…
Wannan shi ne bangare na karshe na hirra da Wakiliyarmu Basira Nakura ta yi da hazikar Malama wadda shahara wajen tarbiyantar tare da ba mata shawarar yadda za su yi zaman aurensu ba tare da wata matsala ba, wato Hajiya Fatima Lawan. Ga dai yadda hirara tasu ta kasance.
Mu nata maganar gyara alhalin shi gyaran nan kowa ya san sai da kudi, to wata macen ma bata samu wadataccen kudin da zaka yi cefane ba ballantana har ta samu abin da za ta gyara jikinta, wata ma ba lallai bane mijin ya bata kudi ba haka nan zai tsallake ya fice ba tare daya bata sisi ba, ko zamu samu wata mafitar a cikin ilimin da Allah ya baki na gyaran mata ko zaki bamu dan kadan dangane da wadancan matan?
Zan nuna mata da kudi dan kadan ma, ynzu masalan miji ya baki dari biyar ta cefane sai kika auna kika ga komai ya hadu a cikin dari hudu da hamsin ko dari hudu, darin nan don kin dauka ya halatta ba ki yi almubazzaranci ba kuma ba kya cikin barauniyar matar da aka ce idan kika dauke wannan darin kika ajiye tsawon kwana biyar kinga nawa kenan ba dari biyar ta hadu ba, to zaki iya zuwa kasuwa ko ki aika a siyo miki dandeban lallanki a samo miki sabulun salo ko sabulun gana, a samo miki kurkum da lemon tsami da kwai a hada su gaba daya ki samu garin hulba cokali daya sai ki samu ruwan dumi ki hade su ki kwaba sai ki shafe jikinki dashi sai ki samu garwashi da dan turaren wuta ki rufa cikin bargo ya gauraye jikinki idan ya bushe sai ki samu auduga da dan man zaitun sai ki rika murzawa zai zube sai ki je ki yi wanka da ruwan dumi da sabulu ba soso to wallahi kika yi wannan miji na shigowa zai hangeki sai yaga yana lale marhabun ina zan kai ki ina zamu shiga.
To kinga wannan abin da ta hada ba fa na lokaci guda bane za ta danyi kamar sati ko kwana biyar tana amfani da shi koma fiye da haka jikinta zai yi kyau zai yi taushi zai yi santsi musamman ma lokacin sanyi.
To Malama yanzu kamar wadda bata da man zaitun fa ta za ta yi?
Shike nan sai ta samu man Basilin ta matsamar lemon tsami saita bar shi an jima kadan saita juya ta juya za ta ga ya dan narke amma kada mace ta ce za ta sa man kuli kuli domin shi baki yake sawa amma idan ta sa wa Basilin lemon ta murza zaki ga jikinta ya yi kyau kamar wata tarwada.
To mun ji bangaren gyaran jiki sai kuma bangaren gyaran mata, shi kuma ya mai karamin karfi za ta yi?
Shima fa ana samun dan alum kadan da lalle kadan idan aka samesu sai a dan cude su idan ba a samu alum ba ana samun bagaruwa itama ‘yar kadan sai a samu zuma amma fa sai an daka su sun yi lukuilukui kamar fulawa sai ta hadesu, ta sa zuma ta kwaba sai ta matsa sai ta hade kafarta tadan dauki kamar minti biyar ma ko kasa da haka sai tasa ruwan dumi ta wanke to insha Allahu in tana yin kamar haka abubuwa yake karawa mai yawa.
To amma na ji ance kamar alimun yana sakar da mace?
Ai dan kadan ake sawa mutane ne basu iya abu ba idan aka ce musu sai sun gunbuda shi kuma in ya yi yawa ma yana dauke ni’imar mace dan kadan ake sawa kamar dan abin masara.
To shi kuma lallan bashi da wata matsala a jikin mace?
A’a lallai bashi da wata matsala,
Kuma akwai ‘ya’yan kargo shima idan ana tsugunawa a ka yi wannan koda mace haihuwa ta yi idan irin gabanta ya yi sakaf sakaf dinnan to yana maste mace.
To shi bawon kargon a haka ake sashi ko ya za a yi masa?
Ana daka shi ne sai ana diban garin kadan ana zubawa a kan garwashin mace ta tsuguna. To ance ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne zaki ga da yawa wani auren yana mutuwa ne don gane da shawarar kawa.
Kin amince da ita kai fada mata sirrinki kun samu matsala da mijinki kin nemi shawarar ta karshe wata ta baki shawarar da zaki kashe auren ki wata ma bayan kin fita ita ita za ta aure mijin naki, yakamata Malama ki yi wa mata Nasiha dangane da wannan
Kuskure ne babban yakamata idan kina da kawa ki kalli suwaye kawayenta idan kawayenta nutsatstsu ne masu sirri masu amana ki yi kawa da ita amma idan kawayenta bankadaddu ne marassa kamun kai karki gaya mata idan marassa amana ne kada ki gaya mata shiyasa aka ce ba a sirri da mutum uku idan kika fada mata ta fadawa wata ya zama ba sirri ba domin ita aminiyar taki tana da aminiya kuma bama komai ake fada ba.
Amma zaki iya ce mata wata aminiyata ta nemi shawara ta a kan abu kaza me kike ganin zance mata danki aunata ki gani idan kinga matar mai boye sirri ce wataran don kince mata ga matsalar ki kina neman shawara ba laifi ba ne.
Amma kuskuren da mata suke yi sirrin mata da miji ba kowa ake fadawa ba idan abu ake nema na shawara ga guraren da Yakamata aje anemi shawara ki ke samu a wajen Malaman addini masu tsoron Allah masu hankali ga su nan mata za su zauna su baki shawara Tamkar ‘yarsu ko ‘yar uwar su amma wata kawa wacce take ba ahalin abin ba ai Allah na cewa, Fas’alu ahalil zikkiri inkuntun la ta’alamu Sadakallahul azim (Ku tambayi ma’abota sani inku baku sani ba) ta ya zaki je ki fadawa kawa bayan alhalin rigimar gidanta ta fi taki wata ma bata da Auren tana can tana ta galudayenta tana neman inda za ta fada, kin saki baki kin ce mata ni wallahi miji na ya takuramin, mai yawan bukata ne tace miki a’a kada ki yadda in ba haka ba zaki lalace da wuri kamar yadda akayi da wata tana kada ta ta fita dama ita irinsa take nema shike nan ka ji da akazo akace ke ya aka yi ta ce gashi-gashi abinda ta ce min ni kuma daman irin haka nake nema amma kai ya ka gani ya ce aiko yanzu na yi mace shike nan suka zo suka dinke yaga cewar duk sanda ya zo shida biyar har takwas ma yana samu ita kuwa da an yi daya na biyun ma da kyar yake samuwa tana nuna cewar ta gaza shike nan ba yadda ta yi sai ta zuba musu ido.
To kinga ita wannan da tona sirri ta samu kanta don haka koda yaushe ba a son mace ta dinga yada sirrinta dana mijinta bai dace ba don haka Allah ya ce, ‘Don me Allah ya ara muku malamai yace Al’umma’u watasatin anbiya don aje a nemesu shawarwari kuma ga wurare nan da za a samu kafofi na bayanai ba irin wannan na shirme ba.
Ko zaki fada mana abubuwa guda goma wanda idan mace ta bi su za ta samu mijinta a tafin hannunta ma’ana za ta mallake shi?
Na daya ta zamo mai gaskiya, na biyu mai tsoron Allah, na uku mai amana, na hudu mai hakuri, na biyar mai Juriya, na shida mai tsafta, na bakwai mai tattali, na takwas mai iya Magana na tara mai girmama iyayen sa, na goma mai ba da kanta a gurin Shimfida
Yadda za ta girgije hade da salo iri-iri bawai ta yi rigijaja ba ya jit a kamar buhun masara, tabbas in mace ta rike wannan za ta mallaki mijin ta.
Muna son mu ji abubuwa guda goma wanda indan mace bata kiyaye su ba za ta iya rasa mijinta.
Na daya karya, na biyu wasa da addininta, na uku ha’inci, na hudu cuta, na biyar wulakanta iyayensa, na shida karya dokar sa
Na bakwai sace masa Abubuwan shine ya hada duk da Ha’inci abinda duk ya batta ba zai same ta a kansa ba, na takwas rashin kawaici, na tara rashin hakuri, na goma kin zuwa Shimfidar sa.
Wadannan abubuwan duk macen da ta riki wancan goma za ta samu mijinta wacce ya sake su kuwa tamkar tasaki mijinta ne
An taba baki wata kyauta ko lambar yabo, wacce ce wadda kika fi jin dadinta kuma kike ganin cewar ba za ki taba manta da ita ba?
To a haka dai kinga ina daga kaina ga su nan kusan guda arba’in amma akwai kyautar da ba zan taba manta wa da ita ba wacce ita ce kyautar da aka bani ta lambar MMR ta Federal din aasa da aka bani, abin da ya sa na kasa manta wa da ita shi ne a lokacin dududu shekara ta talatin da shida ya kasance wanda zai bani a lokacin shi ne Shugaba Obasanjo ne na kasance ni ce mai karancin shekaru don sai da a kayi ta mahawara ma aka yi ta tunanin taya ma akai aka kawo ni don ni kaina ma ban san anata raba lamba saida aka kawo ni na san har kasata ta san da ni alhalin ni ba aikin gwamnati nake yi ba iyakata koyar da matan aure in dan yi musu tafsiri in yi musu abubawa amma aka kira ni nan da nan gwamna ya bada mataimaka mutum goma sha biyu gwamnatin Kano ta bayar su rakana ciki har da Kwamishiniyar mata ita ce Balaraba Bello Maitama muka dunguma muka tafi Abuja to abin da yafi bani mamaki har na kasa manta wa dashi ina shiga aka dinga cemin kadangaren bakin tulu.
An ce sai da aka rike kusan minti talatin wani wanda ba zan kama sunansa ba yana cewa kada a bani a Kano shi kuma mataimakin shugaban kasa da shugaban kasar suna cewa don me ai cancantar ta ce tasa, a lokacin Atiku ne, to wannan abin da aka yi da kuma wanda ya kara bani mamaki wato ana mikawa kowa hannun sa na kalla nace Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un.
Duba dashi ba musulmi bane kuma namiji ne kuma gashi an daukoni an taho dani sannan a lokacin ina shugabar mata ta da’awa ta Jihar Kano gaba daya darika da izala duk suna karkashina a lokacin, na duba naga me zan yi a lokacin sai kawai na koma ina karanta Suratul Yasin a lokacin saida na karanta kafa tara nace Allah ka tsareni daga abinda zan yi na kuskure kafin in je Allah ya bani karfin gwiwa ya ban hannu ni kam na hana shi hannuna wanda ransa ya yi mummunan baci kowa ya gani nan kuwa aka dauki kabbara wannan kabbarar ita ta tayar mar da hankali bai ji dadi ba saboda haka muka taho muna fitowa sai aka ce zamu je koftal party a gidan shugaban kasar lambobin biyu dama aka bamu sai na dauki karamar na makala duk wanda ya zo inka nuna masa lambar sai ya ce mu wuce saboda lambar da aka bamu sun ce zamu iya ganin shugaban kasa kai tsaye muka je yana ta hannu da mutane da aka zo kaina sai ya yi sauri ya razana sai Kwamishiyar mata Balaraba take cewa wai Malama an hadaki da shugaban kasa nace to me nai masa ji kawai na kiyaye hakkin addini nane don a lokacin cewa na yi, gara a karbe lambar da ya yi hannu da shi.
Wannan shi ne award din da ba zan taba mantawa da ita ba saboda ta fito da daraja ta, bama a nan ba har a kasasen duniya saboda an haska ana gani wannan abin shine ya kara samu cewar ashe wani abu ni na yi ban sani ba kuma ni a zuciya ta da naki bashi hannun na yadda ni in dawo babu wannan lambar saboda in kiyaye kaina da mutuncina.
Sai kuma wadanda ba zan manta da su ba cikinsu akwai wani wanda yara ‘yan B.U.K suka bani wanda bayanin da su ka yi a lokacin shima ya yi min dadi haka suma ‘yan Shari’a Law suma.
Na yi matukar jin dadin dukkan su saboda ni ina ganin abu ne nake yi a gida a daki ashe al’umma ta san da shi, kingan su nan dai in kika kalla gasunan ko wanne,To alhamdulillahi.