A cikin rahoton kwamitin tattalin arziki na Nijeriya (NESG) ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe jimillar tsabar kudi na Naira tiriliyan 3.64 wajen bayar da tallafin man fetur tun daga shekarar 2015 har zuwa 2021.
Haka kuma rahoton ya kara da cewa adadin kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe wajen biyan tallafin man fetur ya karu da naira biliyan 307 a shekarar 2015 zuwa naira tiriliyon 1.77 a shekarar 2021.
Wanda ya nuna cewa an samu karin kashi 477 a cikin shekaru shida.
Duka wadannan suna cikin rahoton NESG na tattalin arziki na shekarar 2022 mai taken ‘Sake fasalin tattalin arzikin ta yadda zai inganta’, wanda ya bayyana adadin kudaden da gwamnatin tarayya za ta kashe wajen biyan tallafin man fetur a 2022 duk da barazanar da ake samu na farashin danyen mai a kasuwar duniya.
A makon da ya gabata ne, gwamnatin tarayya ta amince da kashe naira tiriliyan 3 wajen bayar da tallafin man fetur a tsakanin watan Yuli zuwa Disambar 2022.
Tun a farko, aiwatar da dokar man fetur wanda zai kawo karshen bayar da tallafin man fetur zai fara aiki ne a watan Fabrairun 2022, amma sai aka dage zuwa watan Yulin 2022, sakamakon matsinlambar daga kungiyar kwadugo ta kasa (NLC) da kungiyar ‘yan kasuwa (TUC), aka kara watanni 18.
Sai dai kuma NESG ta bayyana cewa rahoton 2021 yana cike da kalubale da ya turnike na shekarar 2022, sakamakon matsalolin da harkokin kasuwanci suka fuskanta saboda annoba da ta sa sai da gwamnatin tarayya ta bayar da tallafi na jinkai ga ‘yan kasa.
An dai kiyasta cewa tattalin arzikin zai karu da kashi 3.2 a cikin wannan shekarar.
Hakazalika, ofishin Akanta Janar na kasa (AGF) ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe naira tiriliyan 4.194 wajen bayar da tallafin mai ga ‘yan kasuwa a tsakanin watan Junairun 2017 zuwa watan Yunin 2022.
Ofishin ya kara da cewa an biya naira biliyan 126.539 a watan Disambar 2017, an biya naira biliyan 691.586 a tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2018, an biya naira biliyan 537.209 a tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2019, an biya naira biliyan 133.625 a tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2020, sannan an biya naira biliyan 1.159 a tsakanin watan Janairu zuwa Disambar 2021, yayin da aka biya naira tiriliyan 1.545 a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin 2022.
Jerin biyan kudaden tallafin yana nan a shafi na biyu a cikin kundin da Daraktan sa ido na ofishin Akanta Janar, Mista Sylba Okolieaboh ya mika wa kwamitin majalisa da ke bincike kan tallafin mai karkashin jagorancin Hon. Abdulkadir Abdullahi.
Haka ita ma ministar kudi da kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahme ta bayyana cewa a duk rana gwamnatin tarayya tana kashi naira biliyan 18.39 wajen bayar da tallafin man fetur.
Ministar ta bayyana hakan ne a gaban kwamitin majalisar wakilai da ke binciken bayar da tallafin mai tun daga shakarar 2013 har zuwa 2022.
A farkon rabin shakarar 2022, kamfanin mai na kasa (NNPC) ya ce ya samu naira tiriliyan 2.6 a wajen sayar da danyan mai.
Sai dai gwamnatin tarayya tana tsammanin za ta kashe naira tiriliyan 6.7 wajen bayar da tallafin mai a 2023. A cikin rahoton NNPC, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe naira tiriliyan 4.838 wajen bayar da tallafin mai a cikin shekaru bakwai har zuwa watan Mayun 2022.
Rahoton ya kara da cewa a duk wata ana samun karuwar farashin tallafin man da kashi 989 daidai da naira biliyan 254.8 har zuwa watan Mayun 2022, wanda aka samu naira biliyan 23.4 a karshen 2015.
Rahoton NNPC ya nuna cewa an kashe naira biliyan 99.00 da naira biliyan 141.63 da naira biliyan 722.30 da naira biliyan 578.07 da naira biliyan 133.73, wadanda aka kashe a shekarun 2016, 2017, 2018, 2019 da 2020, yayin da aka kashe naira tiriliyan 1.573 a 2021.
A 2022 kadai a tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu, an kashe naira biliyan 396.72 wajen bayar da tallafin man fetur.
Majalisar kasa ta amince a kashe zunzurutun kudade da suka kai naira tiriliyan 4 kan bayar da tallafin mai a 2022.
Gwamnatin tarayya ta bakin ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ta kashe naira tiriliyan 10.413 wajen bayar da tallafin mai a tsakanin 2006 zuwa 2019.