Watanni biyu da suka gabata, Shugaba Tinubu ya aike wa da majalisun kasar nan wani kudurin doka da yake neman sahalewarsu, kan wasu kundurori kamar haka;
-Kudurin Dokar Haraji ta Nijeiya ta 2024. -Kudurin Dokar Kula da Haraji – da Kudurin Dokar Samar da Hukumar Haraji ta Kasa (NRS) da kuma Kudurin Dokar Tattara Haraji ta Hadin Gwiwa.
- Sin Ta Zargi EU Da Bayar Da Kariyar Cinikayya Bayan Da Kungiyar Ta Kakaba Karin Haraji Kan Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin
- Kudirin Sake Fasalin Haraji Ya Raba Kan ‘Yan Majalisar Arewa
Sai dai wadannan kudurin dokokin sun gamu da cikas inda kungiyar gwamnonin Arewa sun soki lamarin kundurorin a yayin wani taro da suka yi a Kaduna a watan da ya gabata, musamman na harajin BAT wanda suka ce ya ci karo da wasu muradun Arewa. Wannan ta sa gwamnonin ba wa ‘yan majalisun jihohinsu umarnin yin watsi da wannan kuduri.
Daya daga cikin kudurin dai ya kunshi sauya fasalin harajin BAT ta hanyar rage abin da gwamnatin tarayya ke samu daga kaso 15 zuwa 10.
A gefe guda kuma, kudurin ya kunshi bayanan tsarin yadda za a kasafta harajin da ake samu a kowacce jiha.
Haka kuma majalisar zartarwa ta tatalin arziki, wacce ta kunshi gwamnonin da mataimakin shugaban kasa, ta bukaci shugaban kasa ya janye wannan kudurin daga gaban majalisun kasar nan.
Sai dai shugaban kasa ya yi kunnen uwar shegu da bukatar tasu inda ya ce a bar majalisa ta yanke hukunci.
Jan hankalin da gwamnatin tarayya ta yi kan tsarin
A ci gaba da ganin koma bayan da wasu sassan kasar nan musamman ‘yan siyasar Arewa ke ke yi, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, batun tsarin gyaran harajin da ake yi, an tsara shi ne domin tallafa wa ci gaban da ake fuskanta, ta hanyar magance kalubalen da suka hada da yawaitar haraji, da wasu bukatu, da kuma rage nauyin haraji kan daidaikun mutane da kasuwanci.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, maimakon nuna fargabar rashin gaskiya da masu adawa da tsarin garambawul din suka haifar, ya kamata ‘yan Nijeriya su fahimci cewa manufar ita ce inganta saukin kasuwanci, da saukaka ci gaban tattalin arziki mai dorewa, gami da wadata a’umma.
An samu cece-kuce cewa tsarin da aka gabatar na iya haifar da karancin kudaden shiga ga wasu jihohi, lamarin da zai iya ta’azzara talauci a Arewa.
A wani bayani da ya yi wa jaridar LEADERSHIP, Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Manufofin Kasafin Kudi da Sake Fasalin Haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa sake fasalin ba zai yi illa ga wani bangare na kasar nan ba.
Ya yi nuni da cewa, kashi 5 da gwamnatin tarayya za ta bayar za a iya kebewa domin daidaita kudi saboda a magance duk wata gazawa ga jiha bisa sabon tsarin.
“Wannan yana tabbatar da cewa babu wata jiha da ta fi muni a cikin gajeren lokaci tare da inganta ayyukan tattalin arziki da kuma kudaden shiga ga dukkanin jihohi a cikin tsaka-tsakin lokaci zuwa dogon lokaci,” in ji Mista Oyedele.
Muhimman makasudan sake fasalin harajin sun hada da adadin haraji mai lamba daya, daidaitawa da inganta tsarin shigar da kudaden shiga, karuwar haraji zuwa GDP, da kawar da nauyin haraji kan talakawa.
“Tsarin raba haraji a yanzu kashi 15 ga Gwamnatin Tarayya, kaso 50, na jihohi, da kaso 35 na kananan hukumomi, ana ba da shawarar canzawa ya zamto Gwamatin Tarayya na da kashi 10, Jihohi 55, sai kananan hukumomi kuma su ja kaso 35,” in ji shi.
Wani lamari na daban kuma shi ne, batun sanya harajin kayan masarufi da wasu jihohi ke yi tare da BAT, hakan na kara wa ‘yan kasa nauyi tare da wahalhalu. Amma wannan sake fasalin na nufin dakatar da duk haraji ban da BAT.
A halin yanzu, rabon harajin BAT tsakanin jihohi ya dogara ne akan samun kashi 20, da kashi 50, da kuma kashi 30 na yawan jama’a.
Garambawul din da za a yi wa harajin bisa shawara, wani nau’i ne daban na cire kudi, wanda ya danganta yadda ake samarwa da kuma amfani da shi a maimakon yadda ake fitar da su, wanda a halin yanzu ya zama wata alfarma ce ga jihohi kananan hukumomi shalkwatocin kamfanunnuka.
A karkashin sabon tsarin,
Cire harajin zai kai kashi 60 na rabon BAT, don tabbatar da ingantaccen daidaito da kuma hana kowace jiha neman ba da harajin BAT a matsayin harajin jiha. Irin wannan matakin ba wai kawai zai haifar da raguwar kudaden shiga ga dukkan matakan gwamnati ba ne har ma da sanya wani nauyi ga ‘yan kasuwa.
Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kasa Zacch Adedeji, ya bayyana cewa, idan aka amince da shi a matsayin doka, sabon tsarin zai tabbatar da yin adalci ga jihohi ba tare da dogaro da manyan kamfanoni masu yawa ba kuma za su gane irin gudunmawar da suke bayarwa ga tattalin arziki.
Mista Adedeji ya kuma ba da tabbacin cewa sabon kudirin harajin ba zai zama barazana ga wanzuwar wata hukuma ko ayyuka na gwamnati ba.
Ya jaddada cewa babu daya daga cikin kudurorin haraji guda hudu da ke gaban majalisar dokokin kasar da yake barazana ga wanzuwar kowace hukuma da suka hada da Hukumar Kula Da Harkokin Kimiyya Da Kere-Kere ta Kasa (NASENI), da Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), da kuma Babbar Hukumar Ilimi ka Kasa.
’Yan Majalisa Sun Goyi Bayan Tinubu
Majalisar Wakilai ta ce kudurin dokar sake fasalin haraji na da nufin yin amfani da kudaden shigar Nijeriya wajen inganta daidaito, da samar da yanayin da zai ba da damar zuba jari da kirkire-kirkire.
Kakakin majalisar wakilai Abbas Tajudeen ne ya bayyana haka ne a wani taro mai taken ‘Zaman Majalissar Dokokin Jama’a Kan Kudiri Gyaran Doka’ wanda majalisar ta shirya a Abuja ranar Litinin. Sai dai sun ce a matsayinsu na wakilan jama’a, dole ne ‘yan majalisar su tunkari sauye-sauyen cikin tunani tare da fahimtar tasirinsu ga kowane bangare na al’umma.
Wadannan sun hada da kudurin dokar harajin Najeriya na 2024, wanda ake sa ran zai samar da tsarin kasafin kudin haraji a kasar, da kuma dokar kula da haraji, wanda zai ba da fayyace kuma takaitaccen tsarin shari’a kan duk harajin kasar da kuma rage sabani.
Sauran sun hada da dokar kafa Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Nijeriya, wadda za ta soke dokar Hukumar Tara Haraji ta Kasa da Kuma kafa Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Nijeriya, da kuma dokar kafa Hukumar Tattara Haraji ta Hadin Gwiwa, wadda za ta kafa kotun sauraron kararrakin haraji da kuma mai kula da haraji.
Wadannan a yanzu haka suna gaban majalisar dokokin kasar wanda kuma sun haifar da cece-kuce.
Sai dai kakakin majalisar Abbas ya ce ya kamata haraji ya kasance akan gaskiya da adalci, tare da daidaita bukatun kudaden shiga na jama’a da nauyin da suke dora wa daidaikun mutane da ‘yan kasuwa.
Ya ce har yanzu majalisar ba ta dau takamaimiyar matsaya kan wadannan kudirori ba, domin aikinta shi ne ta yi nazari sosai da tabbatar da cewa sun yi daidai da maslahar al’ummar mazabarta da kasa baki daya.
Muna tare da Tinubu, ba gwamnoni ba – Agbese
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Philip Agbese, ya ce ‘ya’yan jam’iyyar Green Chamber za su marawa shugaban Kasa Bola Tinubu baya kan kudirin sake fasalin harajin da za a yi wanda gwamnonin jihohinsu da ke son a janye dokar.
Agbese, a wata hira da ‘yan jarida a Abuja, ya ce ‘yan majalisar sun dauki kudirin a matsayin wani abin da zai kawo ci gaban tattalin arziki, don haka a shirye suke su yi watsi da kudurorin gwamnonin domin zartar da wadannan kudirori guda hudu.
Taiwo Oyedele
Da yake yi wa ‘yan majalisar tarayya bayani, Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Manufofin Kasafin Kudi Da Sake Fasalin Haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa, kudirin sake fasalin harajin da ake shirin yi, ba wai an yi niyya ne don lalata wani yanki ko wani bangare na kasar nan ba.
Ya ce dokar da aka gabatar za ta tabbatar da inganci ne kawai tare da ba da karin kudaden shiga ga jihohin da ake amfani da kayayyaki da ayyuka.
Shugaban kwamitin shugaban kasa ya jaddada cewa babu wani abin tsoro a cikin kudirorin domin za su samar da maslaha ne ga Nijeriya musamman jihohi da kananan hukumomi. “Babu wani mummunan tunani game da kowane yanki ko wani abu,” in ji shi.
Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano, Abdulmummin Jibrin
A nasa bangaren Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano, Abdulmummin Jibrin, ya roki mutanen Arewa su mara wa kudurin dokar sake fasalin harajin baya da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kawo.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana a ranar Lahadi a cikin shirin talabijin na Channels.
Kofa ya ce kudurin na kunshe da abubuwa da dama da yankin Arewa za ta amfani da su.
“Kudurin ya kunshi wasu matakan ba wa jihohin Arewa kariya daga kowanne irin abin da ka iya cutar da su,”
“Wadannan matakai na da muhimmancin gaske wajen kare muradan yankin Arewa saboda ko da an sake fasalin harajin, Arewa ba za ta fuskanci wani kaluble ba,” in ji Jibrin Kofa.
Mataimakin Kakakin Majalisa
Shima a nasa bangaren, mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, za a binciki kudirin gyaran harajin domin bai wa ‘yan kasar damar tantance su da kuma bayar da shawarwari.
’Yan majalisar Arewa za su kasance masu samar da maslahar kasa – Doguwa
Shugaban Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai na Yankin Arewa, Hon. Ado-Doguwa, wanda ya zanta da manema labarai a wajen taron garambawul din da majalisar ta shirya a Abuja ranar Litinin, ya ba da tabbacin cewa ba za su gaggauta aiwatar da tsarin ba, kuma za su yi adalci ga kudirin da kuma al’ummar Nijeriya ta hanyar yin nazari cikin tsanaki kafin a amince da su.
Dan majalisa daya tilo da ya kalubalanci kudirin Sanata Ali Ndume
A majalisar kuwa, sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar Barno ta Kudu, shi ne jagaba wajen kalubalantar kudurin.
A yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Ndume, ya ce wannan kuduri ya makara domin ba wanda aka tuntuba a kai.
Har zuwa yanzu dai wannan kuduri yana kan matakin karatu na farko a majalisun kasar nan.
Haka ma ko da a watan da ya gabata, kwamitin kudi na majalisun sun zauna da shugaban hukumar tattara haraji na kasa domin duba lamarin.
Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga Ta Kasa FIRS
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Tara Haraji Ta Kasa FIRS, Zach Adedeji, ya bayyana cewa, wannan kudiri zai amfani daukacin jihohi, ba tare da la’akari da yanayin tattalin arzikinsu ba.
LEADERSHIP ta tunatar da cewa shugaba Tinubu ya mika wa majalisar dokokin tarayya wasu kudirori guda hudu na yi wa haraji garambawul ga majalisar dokokin kasar domin tantancewa, biyo bayan shawarwarin da kwamitin shugaban kasa kan sake fasalin kasafin kudi da haraji, karkashin jagorancin Taiwo Oyedele ya bayar.
Haka kuma kungiyar Ulama ta kasa mai shalkwata a garin Kano ta fitar da sanarwar neman a sake nazari a kan shirion yi wa dokar haraji kwaskwarima. Takardfar sanarwa da aka buga a wasu manyan jaridun kasar nan tare da sa hannun shugaban tafiyar Alhaji Aminu Inuwa Muhammad da sakatarensa Injiniya Basheer Adamu Aliyu tare da kuma wasu manyan malamai 25 daga jihohin arewacin Nijeriya. A sanarwsa sun nemi a sake nazari tare da tattaunawa domin a tafi da kowa da kowa a maganar yi wa dokar harajin kwaskwarima dmin kada a yi kitso da kwarkwarta.