Jami’an rundunar ‘yansandan Nijeriya sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da laifin zamba da nufin samar wa mutane aikin gwamnati ta hanyar amfani da jabun takardu daga ofishin shugaban kasa da shugaban jam’iyyar APC na kasa suna karbe ‘yan kudaden jama’a.
Wadanda ake zargin sun hada da Khuzaifa Tafida, Zakari Abdullahi, Abdullahi Baba da Adeyemo Morufu.
- Gobara Ta Laƙume Kadarorin Nairori A Wata Kasuwa A Legas
- An Bar Kasashe Masu Tasowa Da Jidalin Sauyin Yanayi
Wadannan da ake zargin, ana tuhumarsu ne da badakalar karbar kudi da sunan samar wa wadanda suka yaudara aiki a kwalejin ‘yansandan Nijeriya da ke Wudil da sauran hukumomin gwamnatin tarayya.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Abuja, jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce “Daga cikin wadanda ake zargin, Khuzaifa Tafida da Zakari Abdullahi sun buga wata jabun takarda da ta fito daga ofishin shugaban jam’iyyar APC na kasa da wata kuma daga fadar shugaban kasa.”
Rundunar ‘yansandan ta kuma ce, da aka yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifin zargin da ake yi musu domin damfara, inda suke yi wa mutane alkawarin samun aiki a wasu ma’aikatun gwamnati suna amsa kudi.