Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Jamus Toni Kroos ya rattaba hannu akan karin kwantiragin shekara 1 a Real Madrid
Kroos wanda yazo kungiyar daga Bayern Munich a shekarar 2014 ya yi wasanni 417 a kungiyar ta Santiago Bernabeau
Inda ya lashe kofuna 20 ciki har da Uefa Champions League 4,Spanish Laliga 3,Club World Cup 5, European Super Cup 4 da kuma kofin kalubale na kasar Spain 3 a kaka 9 da yayi a Madrid
Kroos ya kara Kwantiragin da zai barshi a Madrid har zuwa 30 ga watan Yuni 2024 inda zasu cigaba da taka leda da sabon matashin dan kwallon Real Madrid Bellingham wanda yazo daga Borrusia Dortmund
A matakin kasa Kross ya taimakawa kasar Jamus lashe gasar kofin Duniya da aka buga kasar Brazil a shekarar 2014