Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta kama wani dan ta’adda mai suna Suleman Iliyasu mai shekaru 28, wanda ya amsa laifin kashe mutane a kalla 15 a wasu hare-haren ‘yan bindiga a fadin jihar.
Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Gambo Isah, ya gabatar da wadanda ake zargin dan ta’addan da ake kira “Yar’bushiya” a gaban manema labarai a hedikwatar rundunar a ranar Talata.
- Zaben Gwamnoni: Wasu Na Kitsa Makarkashiyar Bata Sunan Gwamnan Gombe —APC
- Magoya Bayan Tinubu Sun Gargadi Atiku Da Obi Kan Yi Wa Shari’a Katsalandan
Yar’bushiya ya kuma bayyana cewa ya taka rawa a wasu ayyukan fashi da makami, garkuwa da mutane da satar shanu da aka gudanar a kananan hukumomin Dandume, Faskari, Jibia, Batsari, da Kurfi na Jihar Katsina.
Mai laifin yayi alkawarin sauya hali idan an gafarta masa.
Yar’bushiya, wanda ya yi ikirarin cewa ya fito daga Walawa Asaurara, Sabuwar Ungwa, a karamar hukumar Jibia, a Jihar Katsina, ya kuma bayyana cewa shi mamba ne na kungiyar ta’addanci ta Dankarami.
Dankarami wanda fitaccen dan ta’adda ne, ‘yansanda na nemansa bisa laifin aikata laifukan cin zarafin bil Adama a fadin jihohin Arewa Maso Yammacin Nijeriya.