Shugaban hukumar Karota na jihar kano, Dokta Baffa Babba Dan Agundi, ya gwangwaje wani jami’in Karota da kyautar naira miliyan daya saboda kin amincewa da karbar cin hancin da motocin giya suka ba shi.
Jami’in mai suna, Halilu Kawu Jalo, ya ki karbar cin hancin naira dubu dari biyar 500k biyo bayan kama motocin giya guda biyu wanda suke dauke da giya ta sama da miliyan hamsin.
Shugaban hukumar KAROTA ya bayyna cewa, yana daukar irin wannan matakin ne don kara wa jami’an hukumar kwarin guiwar yin aiki da gaskiya tare da kauce wa karbar cin hanci da rashawa.
Tun da jimawa dai hukumar ta KAROTA karkashin, Baffa Babba, ke dakile sufurin giya zuwa jihar Kano ta hanyar kame motocinsu tare da damka su a hannun hukumar Hisba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp