Daruruwan mutane ne suka amfana da tallafi daga dan majalisa mai wakiltar karamar karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Tallafin da dan majalisa ya bayar ya taba bangarori da dama na rayuwar al’umar karamar hukumarsa ta Sabon Gari.
Baya ga tallafin abinci da dan majalisa ya bayar ga darurun jama’a tuni ya shirya taron koyar da sana’ar dogaro da kai ga daruruwan jama’arsa.
Wakilinmu ya ziyarci dukkan bangaren da ake bayar da horon don tabbatar wa idonsa abin da ke gudana a wajen. Wajen da ake bayar da horon ga daruruwag al’ummar ta karamar hukumar guda 2 ne kuma duk cike yake da mutane
Da yake zantawa da manema labarai, mai taimakawa dan majalisar a bangaren harkar gudanarwa, Kwamred Ishak Adamu (A.D.O) ya bayyana dukkan abubuwan da dan majalisan ya gudanar a ‘yan kwanakin nan wato kafin shigar watan Azumi da cikin watan azumin duk a matsayin tallafi ga jama’arsa karkashin jam’iyarsu ta APC.
Ishak Adamu ya ce, “A yanzu haka mutane 700 ake ba horo maza da mata da samari da har da tsofafi dukkansu ana basu horo ne na koyan kananan sana’o’i kamar yadda za su iya hada alkaki na zamani ko yadda za su hada kek na zamani kuma in sun kammala samun horon dan majalisa zai ba su naira dubu ashiri da biyar (#25,000) ga ko wanne da ya sami horon don yin jali.”
Mataimakin na musamman ya kara da cewa satin da ya gabata ma dan majalisar ya bayar da buhun shinkafa manya da kanana guda (1,500) ga jama’a da tallafin buhun Gero guda (700) ga jama’a don samun albarka.
Ishak Adamu ya tabbatar da cewa duk a satin daya gabata dan majalisa Garba Datti Muhammad Babawo ya saya wa hukumar kula da hadura hanya ta kasa mota ta daukar mara lafiya (ambulance)
“Kuma yanzu haka ya kawo wa dukkan gundumomi (11) da ake da su a fadin karamar hukumar Sabon Gari Fitillar Sola mai haske titi guda (100).”
Ya ce abin mamaki da alfahari shi ne da yawan aikin da shi dan majalisan ya yi a yanzu ya yi su ne bayan an shelanta ya fadi zabe duk da sun ce suna kalubalantar sakamakon zaben a matsayin an tafka magudi ne tsagwaro.
Malama Rukayya Muhammad daga unguwar Gabar Sabon gari tana daga cikin matan da suka sami tallafin bisa hakan, ta nuna Jin dadin horon da ta samu kuma za ta yi amfani da ilmin da ta samu kuma za yi amfani da jarin da aka ba ta domin kula da kanta.
Muhammad Sani daga gundumar Basawa shi ma ya sami tallafin kuma yayi wa dan majalisar fatan alheri da rokon Allah ya ba shi nasara a duk inda ya sa gabansa.