Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Numan/Demsa/Lamurde, Honarabul Kwamoti La’ori, ya kaddamar da ginin ajujuwan karatu uku, a makarantar firamare da ke garin Kwah a karamar hukumar Lamurde a jihar Adamawa.
Da yake jawabi a taron dan majalisa Kwamoti La’ori, ya gode wa Allah da ya ba shi damar cika alkawarin da ya yi wa jama’a lokacin yaÆ™in neman zaben ya ce ba iyawarsa ba ne, ya yi alkawarin ci gaba da yi wa jama’a hidima.
- Hungary Na Sa Ran Ziyarar Xi Za Ta Bude Sabon Babi A Dangantakarta Da Sin
- NNPCL Ya Bayyana Ranar Da Matatar Man Fetur Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki
La’ori ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa tsare-tsaren gwamna Ahamdu Umaru Fintiri, goyon baya domin tabbatar da samun zaman lafiya “idan kun samu bayanai ku sanar da gwamnati domin daukan mataki a kan lokaci”.
Ya kuma yi alkawarin isar da sakon gudanar da aikin babbar hanyar kamar yadda jama’ar yankin suka bukata ga hukumomin da suka dace.
Da ita ma ke jawabi shugabar malamai na makarantar Salome Nicoderius, ta nuna matukar farin ciki da jinjina wa dan majalisar bisa aikin gina ajujuwan da ya yi, ta kuma koka da karancin malamai a makarantar.
A nasa jawabin, tsohon shugaban karamar hukumar Lamurde Bulus Daniel, ya bayyana siyasar fada da cewar dan majalisar da cewa abu ne da ya kamata a ce ‘yan siyasa sun koya.
Ya ce “idan mu ‘yan siyasa za mu yi koyi da irin siyasarka to kuwa za mu cimma nasara, ni da kan ne fitilar siyasa na, zan ci gaba da koyi da kai” in ji Bulus.
Da shi ma ke jawabi sarkin Kwah Mista Nickson Tamuna, ya bayyana dan majalisar a matsayin babban alfahari da kyautar da Allah ya yi wa jama’ar yankin da jihar Adamawa, ya kara da cewa “ka zo mana da alherin da ba zamu taba mantawa da shi ba, muna neman da kayi amfani matsayinka na ganin an gyara mana babban hanyar Lamurde zuwa Karim” in ji sarkin.
Baya ga karrama dan majalisa Kwamoti La’ori da mukamin (Inuwar Kwah), an kuma gudanar da rawar gargajiya na kabilun yankin a lokacin taron na jiya Litinin.