Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jere ta tarayya a jihar Borno, Ahmed Satomi, ya tallafa wa manoma 160 a mazabarsa da naira miliyan 140 domin gudanar da kasuwancin kiwon dabbobi da kiwon kaji.
Da yake jawabi a wajen bikin raba kudaden a Maiduguri a ranar Alhamis, Satomi ya ce, matakin na daya daga cikin kokarin rage tabarbarewar tattalin arziki a Nijeriya da kuma bunkasa ayyukan noma a mazabarsa.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ba Wa Kano Gudunmawar Motocin Kashe Gobara Na Zamani Guda Biyu
- Ramadan: Gwamna Dauda Ya Biya Ma’aikatan Zamfara Kuɗin Hutu Don Kyautata Walwalarsu
Ya bayyana cewa, an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne daga yankuna daban-daban na mazabarsa, kuma sun samu dukkan horon da suka dace domin kiwon.
Dan majalisar ya bayyana noma a matsayin mafita daya tilo ga kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Daga cikin wadanda suka amfana 160, Satomi ya ce, manoma 91 ne suka samu naira miliyan daya kowanne, yayin da sauran suka samu Naira 500,000 kowannensu domin fara kiwon awaki da tumaki.