Hon. Ekene Abubakar Adams, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Chikun da Kajuru a Jihar Kaduna, ya rasu da safiyar Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.Â
Kafin rasuwarsa ya kasance shugaban Kwamitin Wasanni na Majalisar Wakilai.
- Matsalar Karancin Abinci Za Ta Ƙare Nan Ba Da Jimawa Ba – Gwamnatin Tarayya
- Trump Ya Zabi Mai Shekaru 39 A Matsayin Mataimakinsa
Abokinsa Mike Obasi ne, ya tabbatar da mutuwarsa ta wani sako da ya aike wa wakilinmu ta WhatsApp.
Adams, wanda ya kasance tsohon manaja na Kada City FC da Remo Stars, an zabe shi a shekarar 2023 karkashin jam’iyyar LP.
Kasancewarsa masani a harkokin wasanni, ya zama shugaban Kwamitin Wasanni na Majalisar Wakilai har zuwa rasuwarsa a ranar 16 ga Yuli, 2024.
Rasuwar Adams, ita ce ta biyu a Majalisar Wakilai cikin mako guda, bayan rasuwar Hon. Olaide Akinremi (Jagaban) daga Jihar Oyo a ranar 10 ga Yuli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp