Barista Umar Mustapha (Otumba Ekiti), dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar LP a jihar Adamawa, ya janye daga takara, ya kuma goyi bayan takarar ‘yar takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani.
Otumba ya bayyana haka ne a taron manema labarai a ranar Asabar a Yola, wanda ya ce, ya janye daga takara, haka kuma da dukkanin tsare-tsaren yakin neman zabensa sun marawa Sanata Aishatu Dahiru Ahmad Binani, ‘yar takarar gwamnan jam’iyyar APC.
Ya ci gaba da cewa “goyon bayan takarar Aishatu Dahiru Binani ya zama tilas duba da yanayin tafiyar siyasar, kuma tana da duk abinda ake bukata a wajen gwamna, saboda haka ita ta dace da zama gwamna a jihar Adamawa” inji Otumba.