Dan’asabe, mutumin nan da ya yi kalaman da ba su dace ba a kan Babban Asibitin Wudil da aka fi sani da “Wudil General Hospital, Kano State, Nigeria” ya sanar da cewa ya janye kalaman nasa tare da neman afuwa ga wadanda abin ya shafa.
Da kansa a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, duk abin da ya fada game da asibitin a ranar 31 ga watan Yulin 2022, a shafinsa na Facebook da manhajar WhatsApp, ba gaskiya ba ne, kana ya nemi yafiya.
Ga abin da ya fada a sanarwar:
“JANYE KALAMAN DA NAYI AKAN ASIBITIN WUDIL GENERAL HOSPITAL
Ni Danasabe Hassan na janye kalaman dana rubuta akan asibitin Wudil General Hospital da duk wanda ya shafa a cikin asibitin da ragowar kafafen sada zumunta dana rubuta (Facebook da Whatsapp) a ranar 31/7/2022. Duk abinda na rubuta ba haka bane.
Sannan ina baiwa duk wanda abin ya shafa hakuri daga shugaban asibitin zuwa duk wanda ya shafa, kuma na janye maganganun nawa.
Danasabe Hassan”
Kalaman nasa dai sun wanke asibitin daga dukkan abubuwan da ya fada a kansa.