Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai kuya muku yadda ake Dambun Kuskus.
Abubuwan da Uwargida zata tanada:
Kuskus, Zogale, Nama, Kifi, Magi, Gishiri Kori Ko kayan Kanshin da kuke da shi, Tattasai ko taruhu, Albasa:
Da farko za ku tafasa naman sannan ku soya shi. Sai ku gyara Tattasan ko taruhu duk wanda kuka fi so ku jajjaga shi ku dan tafasa sannan ku soya shi.
Sai ku dakko kuskus din ku zuba a wata ruba haka, sai ku zuba wannan naman da kuka soya a kai sai soyayyen tattasan shima ku zuba akai sai ku zuba Magi da Gishiri da kayan kamshi, sannan ku yanka albasa akai, sai ku wanke Zogalan sosai ku tsame masa ruwa ku zuba akai sannan ku gauraya sosai, sai ku dan yayyafa masa ruwa daidai yadda zai ishe shi kun san shi ba ruwa yake so da yawa ba.
Sai ku samu kwando ku zuba shi a ciki idan kwandon yana da manyan kofofi za ku iya samun buhu ku yanka daidai yadda zai dauka sai ku zuba a ciki, kusa a cikin kwandon ko kwalanda, sai ku zoba ruwa a tukunya ko dora kwandon akan tukunya ku dora akan wuta, ku bar shi ya yi ta yi har sai ya turaru.
A ci dadi lafiya.