Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a filin namu na Girki Adon Mata. A yau shafin namu zai kawo muku yadda ake kayataccen dambun shinkafa da kifi da nama.
Abubuwan da uwargida za ta tanada:
Shinkafa, Zogale, Nama, Albasa mai ganye, Mai, Tattasai, Maggi, Kori, Gishiri, Citta da Tafarnuwa.
Yadda ake hadawa:
Da farko za ki gyara shinkafarki ki wanke ta ki tsane ta sai ki barta ta dan bushe, sannan a barzo miki ita a inji sai ki ajiye a gefe. Sai ki wanke namanki ki dora a wuta ki sa maggi, da gishiri da tafarnuwa da citta da albasa. Sannan sai ki zo ki tankade wannan shinkafar da kika barzo ta saboda da tsakin ake amfani.
Sai ki sa ruwa ki wanke tsakin ki tsane shi, ki zuba shi a madambaci ki dora a wuta.
Sai kuma ki gyara zogalenki, ki wanke, ki hada da tsakin sai ki rufe.
Ki tsame namanki, sai ki yanka kayan miyanki ko ki jajjaga duk daya ne ki ajiye a gefe.
Uwargida sai ki duba tsakinki idan ya yi za ki ji yana kamshi shi ne tsakin ya dahu.
Sannan ki sauke ki zuba a roba mai fadi, sai ki zuba soyayyen man da albasa da sauran kayan miya wanda dama kin soya su sai maggi, da gishiri, da kori, da tafarnuwa duk ki zuba sai tare da kifin wanda dama kin gyara shi ki juya ki daddanna sosai saboda komai ya yi dai-dai kar wani waje yafi wani waje dandano.
Sai ki zuba dan ruwan tafasasshen naman ki juye a tukunya ki maida shi wuta ki bashi kamar minti sha biyar, za ki ji gida ya dau kamshin dadi.