Barkanku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai waiwaya ne kan shagulgulan sallah da suke tafiya a yanzu, inda shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko ya shagulgulan sallah ke kasancewa a garinku? Me za a ce game da kalmar ba a yin budurwa ranar sallah? Ko ya mahimmancin zumuncin ‘yan’uwa da abokan arziki ya ke, musamman irin wadda a ke gudanarwa a ranar sallah? Wane bambanci sallar bara da ta bana ya ke da shi?
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Hafsat Sa’eed Jihar Neja:
Game da shagulgulan Sallah yadda na fahimta ta bangarena yadda aka saba haka dai a ke ta lallabawa ba abin da ya canja, shagalin sallah kuma yara na ta nasu shagalin iyaye sun yi iya bakin kokari dan ganin sun fita kunyar yara. Batun yin budurwa ko saurayi ranar sallah wannan zamani ne ya ke sauyawa tunda yanzu samarin da ‘yan matan za ki ga koda kwalliya ko ba kwalliya ko ba sallah ba ce ana son juna a haka, dan haka wannan zamani ya sauya. Zumunci yanada matukar mahimmanci abu ne me kyau a rika gudanar da zumunci ko ba ranar sallah ba, ka kyautata alakarka kodan gobenka.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri, A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya batun shagalin sallah a bana sai dai godiyar Allah tunda Allah ya kawo lokacin muna masu lafiya da rayuwa.To amma batun hidimar sallah ba a cewa komai, domin al’umma suna cikin wani hali na tsadar rayuwa dama tsananin talauci don haka al’umma sun fi maida hankali a kan abinci ba wai sutura ba. To magana ta gaskiya da sallah kowacce budurwar ma ado take iya ado koda kuwa bata yi kafin sallah don haka zai yi wuya mutum ya gane mai tsafta a irin wannan lokaci domin kowace ta kure adaka wajen kwalliya da ado domin lokaci na murna da farin ciki. To zumunci abun mai matukar muhimmanci duba da yadda addinin mu ma na musulunci yayi jan hankali a kan ake raya zumunci domin abu ne ya ke sa kauna da shakuwa a tsakanin al’umma ‘yan uwa ko kuma abokan arziki dama sauran al’ummar gari, don haka abu ne mai matukar muhimmanci musamman irin wannan lokaci na bukukuwan sallah. To magana ta gaskiya bambancin dake tsakanin sallar bara da bana ita ce wadata domin a bara akwai saukin rayuwa ba kamar bana ba da’ake fama da hauhawar kayan masarufi, tsadar rayuwa dama tsananin talauci a tsakanin al’umma, don haka sai dai kawai mu yi addu’ar Allah ya yi mana mafita daga wannan matsala ta tsadar rayuwa.
Sunana Hassana Sulaiman, Hadejia A Jihar Jigawa:
Alhamdulillah da farko za mu ce game da shagulgulan bikin sallah a garin mu da kuma unguwar mu, duk da kasancewa ma dai sallar wasu daga cikin bakin da ke shigowa garuruwan su ma asali wasu basu samu damar zuwa ba kasancewar yanayin tsadar rayuwar da kuma na man fetur da yaki ci yaki cinyewa, wannan ya sa wasu daga cikin al’ummar da suka saba zuwa gida dan gudanar da bikin sallar basu samu halarta ba. Eh! to, a kan kalmar da mafi yawan al’umma ke amfani da ita na cewa ba a yin budurwa ranar sallah ko ba a yin saurayi ranar sallah idan muka dauki maganar ta wata fuskar sun yi gaskiya, kasancewa wasu kan da gaaske ne basa yin adon da kwalliyar sai ranar sallar kuma fa wannan ba iya bangaren matan bane a’a kowane bangaren ne na mazan da matan, da wannan ne yasa wasu ke ganin cewa wannan kalmar za ta iya yin tasiri ga duk wani da yayi budurwa ko saurayin ranar sallar, amma kuma wasu abin ba haka yake ba ana iya dacewa fiye da yadda mutum ke tunani ma. Zumunci kan abu ne mai matukar muhimmanci wanda addinin mu ya kwadetar da mu kasance masu sada shi tsakanin ‘yan uwa da ma abokan arziki, kuma irin wanda ake gudanarwa a bikin sallah abun yana da matukar tasiri ga duk wani da ka ziyarce shi a daidai wannan lokaci yana jin dadin hakan da kuma yin farin ciki sosai wanda a fuskarsa za ka iya fahimtar hakan. Gaskiya akwai bambanci kan sosai ga sallar bara da a ka gudanar da kuma wannan ta bana da a ke gudanarwa, don kuwa idan muka duba bara samun kudaden da al’umma ke yi ya dan fi na bana kuma yanzu bana abubuwan duk sun sauya kama daga siyan duk wani nau’i na sutura da kayan masarufi kayan yin ado da duk wani abun da ka siye shi bara to fa bana kudinsa ya ninku kusan ninki uku zuwa hudu kun ga kuwa bara ta dan fi sauki a kan bana da kusan kaso talatin cikin dari, sai dai Allah ya kawo mana saukin rayuwar nan.
Sunana Comrade Anas Bin Maleek Achilafia Yankwashi, A Jihar Jigawa:
Shagalin karamar sallah a bana, daga nan gundumar mu ta ACHILAFIYA, sai dai mu ce Alhamdulillah, iyaye sun yi bakin kokarinsu, dan ganin sun saka farin ciki a zukatan iyalansu, duba da yanayin tattalin arzikin kasa, da halin al’umma ke ciki. Batun ba a zaben budurwa ranar sallah kam haka batun yake, domin da yawan ‘yan mata, suna kure adakarsu ta gayu ne, ranar sallah, idan kuwa ta wuce, shakka babu idan ka ganta, ba za ka iya shaida ta ba. Shiyasa ni ko gwada zaben budurwa ranar Sallah ba na yi. Zumunci abu ne mai muhimmancin gaske, Saboda muhimmancinsa ma har Allah madaukakin sarki, da manzonsa sai da suka yi mana umarnin sada shi, sannan kuma ya zama al’ada ce ga hausawa manya da kananan yara ziyartar ‘yan uwa da abokan arzuka, domin jaddada shi. Hauhawar farashin kayayyaki na daga cikin abin da ya bambanta bikin sallar bana, da ta bara, kasancewar an cire tallafin man fetur wanda shi ne kasa ta dogara da shi a cewarsu, sai a ka samu tashin gwauron zabi na dukkanin kayyakin bukatu na rayuwar yau da kullum.
Amina Umar, Jihar Kano, Gwale LGA:
Shagalin sallah
Gaskiya dai shagalin sallah yana kasancewa yadda a ka saba duk shekara sai dai tsadar rayuwa data sauya wasu abubuwan. Eh! wasu suna yin budurwa ranar sallah, amma ni dai ban taba yin saurayi da sallah ba. Azumin bayan sallah yanada mahimmanci sosai saboda Annabi Muhd (s.a.w) yayi kuma dama shi muke koyi, ya kamata kowa yayi. Akwai bambanci sosai tsakanin bara da bana, rayuwa ta kara tsada fiye da waccen shekarar. Ina taya ‘yan uwana musulmai murnar zagayowar shagalin bikin sallah Allah ya maimaita mana.
Sunana Alhaji Aminu Garba Halliru, Jihar Kano:
Allahamdulilah kowa da kawo yana farin ciki ana ta nishadi kamshin turare ta ko ina yara suna ta wasa suna jindadi ga abinci ta ko ta ina muna godiya ga Allah (SWT) da ya kawo mu wannan sallar mai Albarka. Gaskiya ni ban taba yin budurwa ranar sallah ba, Eh! to, abin da zan iya tsokatawa shi ne; kowa ya san cewa ba wanda ya ke barin kansa da kazanta ranar sallah, hakan ya saka cewa mata da maza za su yi ado na burgewa saboda su ja hankalin al’umma, hakan ya sa ba a gane kazami ko kazama, indai kaj e ka taya baka san yadda take ko yake ba to, gaskiya akwai kura. Shi zumunci dole ne a adinin muslimai saboda Allah (SWT) yana cewa; mai yanke zumunta ba zai shiga Aljanna ba to, kun ga ko ba sallah zumunci yana da fa’ida musaman da sallah saboda kowa yana cikin farin ciki za a ga ‘yan uwa da abokan arziki, kuma har a shirya wani taron sallah mai ban nishadi wanda za ka hadu da wanda baka sani ba. Sallah dai Sallah ce sai dai a gurin wani wannan tafi wani kuma ta bara to, ni dai gaskiya sallar bara tafi dadi duba da tsadar rawuya da talauci dake damun al’umma a yanzu sai dai hamdala kawai.
Sunana Rahma Ahmad, Jihar Kano:
Shagulgulan sallah a garinmu sun kasance ana gudanar da su cikin zaman lafiya da nishadantarwa. Eh! wannan batun gakiya
ne a nawa ganin, domin wadansu matan sai ranar sallah su ke fitowa fes! wadansu ma ba a iya gane su ranar sallah, saboda basu saba yi ba sai ranar sallah, toh idan mutum ya zabi budurwa ranar sallah kun ga bai sani ba ko me tsafta ce ko mara tsafta. A gaskiya dai zumunci yanada matukar mahimmanci a kodayaushe, saboda ya na amfanarmu a kowanne yanayi, ana son a rika ziyartar ‘yan’uwa da abokan arziki domin nuna mahimmancinsu. Ni a gaskiya ban ga wani bambanci ba domin kowa yana kokarin ganin ya fito ya yi kyau, sai dai tsadar rayuwa ta hana hakan. Ina gaida Mamana, Babana, Kanwata da Kanina, Kawayena na makarantummu da fatan sun yi sallah lafiya.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kan Rano LGA:
Alhamdulillah komai yana tafiya yadda ya kamata kowa yana cikin farin ciki gashi muna cikin walwala. Wannan hausar malan bahaushe ce kawai amma zabar budurwa ranar sallah hakan ya dace duba da idan ka ga mace bata yi kyau ba to daga kai ne koda kun yi aure. Gaskiya ban taba yi ba duba da ban yi irin wannan kule-kulen ‘yan matan ba. Ai muhimmancinsa ba shi da adadi domin zumunci mai yanke shi ma zunubi ya ke samu balle kuma gashi na sallah. Bambancinsa yana da yawa amma wanda yake ya fito a fili shi ne na rashin ziyarce-ziyarce duba da tsadar mai wanda shi ne ya samar da tsadar ababen hawa, amma du da haka Alhamdulillah, wasu suna iya nasu kokarin na ganin sun kai ziyarce-ziyarce yadda a ka saba.
Sunana Umar Babanyaya Sabongida Kafin-Hausa, A Jihar Jigawa:
Batun shagulgulan karamar sallah na wannan shekara a garin mu na sabongida sai dai mu ce Allahamdullah, domin dai ganin irin yanayin da sallar ta zo mana na bana, wai aljannar waina sama zafi kasa zafi, amma mun gode Allah daya nuna mana ita cikin koshin lafiya. Yin budurwa ranar sallah da wasu mutane ke yi ni a ganina rashin fashimtar lokacin daya dace masu yin ‘yan mata ranar sallah suke yi ranar, domin dai babu wani lokaci da mace za ta yi kwalliyar fita daga kamanninta irin ranar ta sallah, Toh ni dai Baban’yaya tunda nake ban taba yin budurwa ranar sallah ba, saidai kuma yadda suke kwarkwasa da yin kwalliyar yana matukar burge ni. Hakika zumunci yanada matukar mahimmanci ga ‘yan uwa kwarai duba da yadda irin ranakun Sallar Juma’a da sauran wasu ranaku masu mahimmanci yara da manya kan ziyarci ‘yan uwa da abokan arziki domin sada zumuncinsu hakan na kara farfado da zumunci kwarai da aniya muna fatan Allah ya dafa mana. Za mu iya cewa an samu bambancin bikin sallar bara da kuma ta bana duba da irin halin matsi da ake fuskanta a irin wannan lokacin da kuma tsadar kayayyaki, don haka muke ganin an samu bambanci kwarai ko ta fuskar walwala ga jama’a.
Sunana Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki, Jihar Kano:
Assalamu alaikum Barka da Sallah karama Allah ya karbi ibadunmu. Shagulgulan sallah a garinmu Kano Alhamdulillah komai na tafiya cikin aminci. Abun da ya sa hausawa ke cewa ba a budurwa ranar Sallah shi ne saboda kowa yana ado, bayan sallah kuma ka gansu babu fasali, amma ni gaskiya ya zan yi yin budurwa ranar Sallah. Domin ya danganta da mai yin budurwar da kuma wace ce budurwar. Zumunci na da matukar muhimmanci ga al’umma baki daya domin yana kyautata alaka tsakanin musulmi da kyautatawa, da kuma lada wajen Allah (SWT). A gaskiya sallar wannan shekara ta zo da sauye-sauye da dama sai dai Allah ya bamu dacewa. Ina mika sakon gaisuwata ga dukkanin al’ummar musulmi bakidaya da fatan an yi Sallah lafiya.