Da yammacin yau Alhamis ne shugaban hukumar watsa labarai ta ma’aikatar tsaron kasar Sin, kana mai magana da yawun ma’aikatar Wu Qian, ya yi bayani kan yadda ake gudanar da dandalin zaman lafiya da tsaro na Sin da Afrika karo na 3, a gun taron manema labarai da aka gudanar.
Wu Qian ya ce, a yayin taron, mahalartan sa sun cimma matsaya daya kan shawarar tabbatar da tsaron duniya, da karfafa hadin kan Sin da Afrika, da zurfafa mu’ammala bisa jigon dandalin. Kaza lika manyan abubuwa mafi jawo hankali a wannan karo su ne, na farko ana matukar fatan samun zaman lafiya, na biyu kuma ana matukar bukatar samun bunkasuwa, na karshe kuma ana samar da matakai masu dacewa don hadin gwiwarsu.
Game da mu’ammalar sojojin Sin da Afirka ta kudu, Wu Qian ya ce, ana cikin lokaci mafi kyau a tarihi, kuma sojojin kasashen biyu sun cimma nasarar hadin kai mai armashi, a fannin mu’ammalar manyan jami’ansu, da atisayen soja, da fasahohin kera na’urori, da kiyaye zaman lafiya a duniya da dai sauransu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp