Kamfanin albarkatun Mai na kasa (NNPCL) ya ce tattauna a halin yanzu na ci gaba da tafiya kan sabuwar kwangilar cinikayyar danyen mai a kan naira a tsakaninsa da matatun mai na cikin gida.
Kamfanin wanda ke maida martani kan rahoton da ke cewa ya dakatar da hada-hadar cinikayyar danyen mai a tsakaninsa da matatun mai da suke cikin gida, lamarin da ya janyo dillalai, masu ruwa da tsaki da ‘yan Nijeriya suka dukufa nuna ra’ayoyinsu mabambanta.
- Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta Ware Mata – Bincike
- Hajjin Bana: NAHCON Za Ta Fara Jigilar Maniyyata A Ranar 6 Ga Mayu
Hada-hadar saye da sayar na danyen mai kan naira wanda ya kwashe tsawon watanni shida ana gudanar da shi, an labarto cewa ya zo karshe, inda hakan ya janyo fargabar yiyuwar karuwar farashin kudin man fetur da kuma sake janyo tashin dala a kan naira.
Idan za a tuna dai, a watannin baya ne Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci a sayar da danyen mai ga matatar mai na Dangote a kan naira domin saukaka farashin mai a cikin kasar nan.
A watan Oktoba na shekarar 2024, majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da cewar ake sayar da gangar danyen mai 450,000 a kan naira ga matatun cikin gida, wanda matatar mai ta Dangote ta kasance nan gaba a wannan harkar.
Rahotonni sun yi nuni da cewa kulla yarjejeniyar cinikayyar danyen mai a farashin an kulla ta ne a watan Oktoba na 2024 kuma da tunanin zai kare a watan Maris din 2025.
A tsawon wannan lokacin, an samun karancin yawan danyen man da kamfanin ke samar wa matatar na Dangote.
Takardar da aka yi nazari a karshen watan Janairu ta nuna cewa a watan Fabrairun 2025, an ware shirin samar da mai na kan naira zuwa jirgin dakon mai hudu ne kawai, rukuni hudu zalla, kuma a watan Maris, dakon man biyu ne kawai aka yi da ya kai ganga 950,000 (ganga miliyan 1.9 ga watan). Wannan yana wakiltar rabon ganga 61,290 a kowace rana kasa da makasudin 385,000 bpd a karkashin tsarin.
Karancin samun danyen mai ya tursasa wa matatar man Dangote garzaya wa kasashen waje domin neman danyen man. A baya-bayan nan kamfanin ya samu gangar danyen mai miliyan 12 daga Amurka.
Duk da dai har yanzu matatar Mai ta Dangote ba ta fito a hukumance ta yi bayani kan karewar yarjejeniyar cinikayyar danyen mai din ba, amma wata majiya daga matatar ya tabbatar da cewa zancen ya kare, sai dai majiyar ba ta ba da cikakken karin haske ba.
Sai dai, kakakin kamfanin NNPC, Olufemi Shoneye yayin da ke fashin karin haske kan batun karewar hada-hadar cinikin, inda ya ce, “Bar na fayyace wannan lamarin, daman an kulla yarjejeniya ce na watanni shida, ya danganci wadatar danyen mai, kuma zai kare ne a karshen watan Maris na 2025.
“Tattaunawa na ci gaba da gudanar kan yadda za a kulla sabuwar yarjejeniya.
“A karkashin wannan yarjejeniyar, NNPC ya samar da danyen mai sama da ganga miliyan 48 ga matatar Mai ta Dangote tun watan Oktoban 2024.
“A takaice, NNPC ya samar da danyen mai ganga miliyan 84 ga matatar tun lokacin da ta fara aiki a shekarar 2023.
“NNPC ya himma wajen samar da danyen mai ga matatun mai na cikin gida a bisa tsarin yarjejeniya da sharuddan da aka cimma,” ya shaida
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp