Alhaji Aliko Dangote, attajirin mafi kuɗi a nahiyar Afrika, ya fara neman lasisin gina tashar jiragen ruwa mafi girma kuma mafi zurfi a Nijeriya, a garin Olokola da ke jihar Ogun, kamar yadda rahoton Bloomberg ya bayyana.
Sabuwar tashar jirgin ruwa ta Atlantika za ta kasance mai matuƙar tasiri ga harkokin sufuri da fitar da kaya na kamfanin Dangote, musamman wajen tallafawa manyan masana’antunsa na takin zamani da sinadarai. An shirya gina tashar ne kimanin kilomita 100 daga masana’antun Dangote da ke Lagos.
- Matatun Man Fetur Na Nijeriya Ba Za Su Ci Gaba Da Aiki Yadda Ya Kamata Ba – Dangote
- Dangote Ya Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 820
A wata hira da aka yi da shi, Dangote ya tabbatar da cewa kamfaninsa ya miƙa takardun buƙatar fara aikin a ƙarshen watan Yuni, yana mai cewa: “Ba wai muna son mu yi komai da kanmu ba ne, amma irin wannan babban zuba jari na iya zaburar da wasu masu hannu da shuni su ma su shiga.”
Yanzu haka Dangote na amfani da wata ƙaramar tashar jirgi da ke kusa da matatar mai domin fitar da takin zamani da kayan aiki masu nauyi. Amma wannan sabon gini zai haɗa dukkan ayyuka na fitar da kaya da sufuri, kuma zai iya fafatawa da tashar jiragen ruwa ta Lekki, wadda Sin ke tallafawa, kuma aka kammala a shekarar 2023.
Baya ga takin zamani, Dangote yana da shirin fara fitar da iskar gas ta LNG daga Legas, wanda zai haɗa da gina bututun gas daga yankin Niger Delta zuwa gaɓar teku. “Muna so mu yi wani babban aiki da zai fi na kamfanin NLNG na yanzu,” in ji Dangote.
A cewarsa, irin wannan manyan ayyuka na iya sauya yanayin tattalin arzikin Afrika idan aka tunkare su da hangen nesa da ƙarfin gwuiwa. Ya bayyana a baya cewa kamfaninsa na shiri don samar da dala biliyan 30 a shekara mai zuwa, tare da burin zarce ƙasar Qatar a matsayin mafi girman mai fitar da urea a duniya cikin shekaru huɗu masu zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp