Kamfanin Dangote Cement Plc ya zuba fiye da dala miliyan 280 domin tallafa wa shirin gas na CNG da Shugaba Bola Tinubu ya ɓullo da shi, wanda ya shafi samar da hanyoyin mai masu rahusa da kuma marasa gurɓata muhalli a Nijeriya.
Wannan mataki na daga cikin ƙudirin Tinubu na samar da kayan aikin amfani da CNG a cikin ƙasa baki ɗaya, wani ɓangare na tsarinsa na samar da makamashi mai tsafta. Shugaba Tinubu ya umarci raba kayan sauya motoci miliyan 1 kyauta ga motocin haya masu ɗaukar mutane da kayayyaki.
- Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Sauke Ministoci 6 Tare Da Sauya Wa 10 Ma’aikata
- Tinubu Ya Naɗa Sunday Dare a Matsayin Mai Magana Da Yawunsa
A wani taron kwanan nan, Shugaba Tinubu ya bayyana muhimmancin amfani da iskar gas a Nijeriya wajen harkar sufuri, yana mai cewa CNG na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arziki kuma zai kawo sauyi a harkar sufuri da makamashi a ƙasar.
Manajan Darakta na kamfanin Dangote, Arvind Pathak, ya sanar da shirin kamfanin na sauya motocinsa zuwa CNG, wanda zai fara da zuwan sabbin motoci 1,500 masu amfani da CNG kawai. Zuwa tsakiyar shekarar 2026, Dangote na fatan amfani da CNG a mafi yawancin ayyukansa tare da haɓaka cibiyar tallafin mai ta CNG. Pathak ya bayyana sadaukarwar kamfanin ga manufar makamashi mai tsafta, inda aka kammala gina cibiyar cika mai ta CNG a Obajana, yayin da ake ci gaba da ginawa a Ibese.
Shugaban rukunin kamfanin Dangote, ya bayyana cewa jarin kamfanin na CNG yana da alaƙa da burin Nijeriya na cimma ƙudirin rage fitar da gurbataccen iska zuwa sifili nan da shekarar 2060.