Matatar man Dangote ta sake rage farashin man fetur zuwa Naira 820 kan kowace lita, daga Naira 840 da ake sayarwa a baya.
Wannan sabon farashi zai fara aiki nan take.
- Tinubu Ba Zai Yarda Hayaniyar Siyasar 2027 Ta Ɗauke Masa Hankali Ba – Ministan Yaɗa Labarai
- Igbo Ne Ke Aikata Laifuka A Kudu, Ba Fulani Makiyaya Ba – Gwamna Soludo
A makon da ya gabata, matatar ta rage farashin daga Naira 880 zuwa Naira 840.
Yanzu kuma ta ƙara ragewa zuwa Naira 820.
Yayin da matatar ke tabbatar da samun isasshen man fetur a ƙasa, ‘yan kasuwa sun nuna sha’awar siyan man daga matatar Dangote saboda ingancin man da kuma tabbacin wadatarsa.
Mai magana da yawun matatar Dangote, Mista Anthony Chiejina, ya tabbatar da rage farashin a Legas.
Ya ce, “Farashin man fetur ya ragu daga Naira 840 zuwa Naira 820 kan kowace lita.”
Ya bayyana cewa rage farashin da aka yi a baya zuwa Naira 840 ya faru ne sakamakon hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya sanadiyyar rikicin da ya auku a Gabas ta Tsakiya.
Kamfanonin da ke haɗa kai da Dangote irin su MRS, Heyden, Ardova (AP), Hyde, Optima, da Techno Oil za su fara sayar da fetur a sabon farashin.
Haka kuma, wasu sabbin kamfanonin da ke dillancin mai sun shiga jerin masu rarraba man Dangote.
Kamfanonin sun haɗa da: TotalEnergies, Garima Petroleum, Sunbeth Energies, Sobaz Nigeria Ltd., Virgin Forest Energy, Sixxco Oil Ltd., N.U. Synergy Ltd., Soroman Nigeria Ltd., Jezco Oil Nigeria Ltd., Jengre, Cocean, Kifayat, Triumph Golden, Sifem Global, Riquest, da Mamu Oil da sauransu.
Matatar Dangote ita ce mafi girma a nahiyar Afirka kuma ɗaya daga cikin manya a duniya da ke tace ɗanyen mai.
Dangote ya kashe sama da Naira biliyan 720 wajen shigo da motoci 4,000 da ke amfani da iskar gas domin rarraba man fetur a faɗin Nijeriya.
Dangote ya ce zai ɗauki nauyin sama da Naira tiriliyan 1.07 na kuɗin jigilar mai a duk shekara.
Wannan shiri zai taimaka wa masu ƙanana da matsakaitan masana’antu miliyan 42 ta hanyar rage kuɗin makamashi da ƙara yawan ribarsu.
Haka kuma, zai rage yawan kuɗin dakon mai da dilallai ke biya, wanda hakan zai iya sa farashin mai ya sauka a gidajen mai tare da rage hauhawar farashin kayayyaki.
A baya, Dangote ya sanar da shirinsa na fara kai fetur da dizil kai-tsaye zuwa matatun mai da masana’antu daga ranar 15 ga watan Agusta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp