Shugaban Kamfanin Dangote kuma attajiri mafi arziƙi a Nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya aike wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu wasiƙa, inda ya nuna gamsuwarsa kan irin sauye-sauyen tattalin arziƙi da kuma hangen nesa wajen samar da manyan ayyukan ci gaban ƙasa.
A cikin wasiƙar da ya aike masa a ranar Laraba, Dangote ya bayyana jin daɗinsa da godiya bisa yadda Shugaba Tinubu ya samar da ababen more rayuwa, musamman fara aikin ginin Bar Beach, Victoria Island, da ke Jihar Legas.
- Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo A Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo
- Buhari Ba Mutum Ne Mai Son Abun Duniya Ba – Gowon
A cewarsa, wannan yanki wanda yake cibiyar kasuwanci na fama da ambaliya tun daga shekarar 2008, amma sabon aikin zai inganta harkoki a yankin.
Dangote ya ce: “Hangen nesanka da matakin da ka ɗauka sun bayyana a yanzu idan aka kwatanta da abin da ya faru a Kerr County, Texas, Amurka, inda mutane sama da 100 suka rasu sakamakon mummunar ambaliya. Abin da ka yi ya ceci rayuka da dukiyoyi da dama a nan Nijeriya.”
Ya kuma jinjina wa Tinubu bisa nasarar gina Eko Atlantic City, wani sabon birni da aka gina a Legas.
Wannan sabon birni na da ganuwa mai tsawon kilomita 8.5 da zai kare Legas daga ambaliyar ruwa, kuma yana da gidaje, ofisoshi da wuraren kasuwanci da na nishaɗi.
Dangote ya ce wannan aiki yana daga cikin manyan abubuwan tarihin da Shugaba Tinubu zai bari.
Hakazalika, ya nuna godiyarsa bisa fara aikin titin gaɓar teku daga Legas zuwa Kalaba da kuma aikin titin Sakkwato zuwa Badagry, waɗanda za su inganta sufuri da tattalin arziƙi a faɗin ƙasar.
Ya kwatanta hangen nesan Tinubu da yadda ƙasar Netherlands ta kasance wajen samar da muhallai a cikin ruwa don raya birane.
Dangote ya ƙara da cewa kamfaninsa na jin daɗin irin goyon bayan da gwamnati ke ba shi wajen sauƙaƙa kasuwanci da bunƙasa tattalin arziƙi.
Ya ce Nijeriya na fuskantar barazanar ambaliya, wanda hakan ya sa gidauniyarsa ta Aliko Dangote Foundation ke shirin ƙaddamar da wani Asusun Tallafa wa Matsalar Sauyin Yanayi domin taimaka wa al’ummar da ambaliya ke shafa a faɗin ƙasar.
Dangote ya roƙi Allah Ya bai wa Shugaba Tinubu hikima da nasara wajen jagorantar Nijeriya, sannan ya tabbatar masa da goyon bayan kamfaninsa da dukkanin ‘yan kasuwa masu kishin ci gaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp