Tsohon gwamnan Jihar Gombe kuma daya daga cikin ‘yan tawagar siyasa na Gwamnan Jihar Ribas, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya yi watsi da alkiblar kungiyar ‘yan ra’ayi masu kulli a rai na jam’iyyar PDP wanda suke karkashin tawagar gwamnonin G-5 na Wike.
LEADERSHIP ta labarto cewa Ibrahim Dankwambo fitaccen mamba ne a tawagar su Wike, wadanda suka dauki tsawon lokaci su na tataburza da shugaban jam’iyyar PDP na kasa da dan takararta Atiku Abubakar na tsayawa kan matsayar su na cewa dole kuma tilas sai Dakta Iyorchia Ayu ya sauka daga matsayin shugaban jam’iyyar.
A kan hakan ne mambobin kungiyar sun Wike suka shelanta ficewa daga kwamitin yakin zaben Atiku/Okowa su na masu nanata bukatar fa sai an kori Ayu kawai.
Kazalika, kwatsam da mamaki, sai kuma tsohon gwamnan Jihar Gombe Dankwambo ya yi tarayya da Atiku tare da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Gombe inda suka hadu a ranar Litinin a wajen gangamin yakin neman zaben Atiku da aka gudanar a jihar Gombe.
Dankwambo dai an gano shi tun daga filin jirgi na jihar Gombe inda suke ta tarbo manyan baki zuwa wajen taron gangamin, daga nan har ma ya yi magana da masoya da magoya bayan jam’iyyar.