Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa a ko’ina a duniya dansanda yana wakiltar al’umma da kuma gwamnati, sannan akwai bukatar a girmama shi.
Osinbajo ya bayyana hakan ne a madadin shugaban kasa lokacin da ya wakilce shi a wurin bayyana rahoton hukumar da ke kula da harkokin ‘yansada na shekara-shekara, karkashin jagorancin makaddashin shugaban hukumar, Clara Ogunbiyi wanda ya jagorancin tawagar zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Hukumar ta gabatar da rahotanta na shekara kamar yadda sashi na 17 da dokokin ‘yansanda ta shekarar 2001 ta tanada.
A cikin sanarwar da mashawarcin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ya fitar, ya bayyana cewa a kowacce hanya dansandan Nijeriya aikinsa shi ne tsare al’umma kuma yana wakiltar mutane ne.
“Bisa dalilai masu yawan gaske, mutane suna daukan aikin dansanda a matsayin aikin da gwamnati ta gudanar, domin haka yana da matukar muhimmanci ‘yansanda su gudanar da ayyukansu yadda ya dace.”
A nasa jawabin, makaddashin shugaban hukumar kula da harkokin ‘yansanda ya ce ko sakka babau gwamnati tana aiki da tsarin dokar kasa. Ya ce a matsayin su na hukumar da ke hukawa da harkokin ‘yansanda za su tabbatar da cewa ana amfani da abubuwan da tsarin mulki ya shimfida.
Sauran mambobin tawagar hukumar kula da harkokin ‘yansanda sun hada da Hon. Lawal Bawa da Hon. Hajiya Hadiza Muhammad da Hon. Austin A. Braimoh da dai sauransu.