Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (DAPPMAN) ta zargi Matatar Dangote da kawo cikas ga kasuwar mai biyo bayan rage farashin fetur.
Matatar ta sanar da cewa lita ɗaya ta fetur za ta kasance kan Naira 841 a Legas da Kudu maso Yamma, da Naira 851 a Abuja, Edo da Kwara, maimakon Naira 865 da ake sayarwa a baya.
- Yadda Wani Ya Kashe Ƙaninsa, Ya Ɓoye Gawar A Duro
- An Kaddamar Da Tashar Watsa Labarai Ta CMG A Chengdu
DAPPMAN ta ce sauke farashin ana yin sa ne a lokutan da zai cutar da sauran ’yan kasuwa da suka riga suka kawo kaya.
Haka kuma, ta zargi Dangote da sayar wa ƙasashen waje mai yayin da ake lafta wa ’yan Nijeriya farashi mai tsada.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa ba Dangote kaɗai ne ke samar da mai a ƙasar nan ba, domin ko rabin man da Nijeriya ke buƙata ba ya iya samarwa.













