Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a rubu’in farko wato daga watan Janairu zuwa Maris na bana, darajar wadannan bangarori ta karu da dalar biliyan 452.5 a wadannan watanni uku, wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokacin bara, kana adadin ya kai kashi 10.4% bisa na dukkan GDPn kasar.
Nagartacciyar bunkasar wadannan sana’o’i na nuna goyon baya na tsarin habaka bukatu cikin gidan kasar da tafiyar da tattalin arzikin al’umma ba tare da tangarda ba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp