Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayyar kasar Sin He Yadong, ya ce a shekarar 2023 da ta gabata, darajar jimillar hajojin shige da fice daga yankunan bunkasa tattalin arzikin Sin ta kai yuan tiriliyan 10, kuma cikin wannan adadi yawan kudaden ketare ya kai dalar Amurka biliyan 39.5. Dukkanin alkaluman biyu kuma, sun kai sama da kaso 24 bisa dari kan adadin alkaluman da ake da su a kasa baki daya.
A wani bangaren kuma, game da furucin kasar Amurka na cewa za ta kakabawa wasu kamfanonin kasar Sin takunkumi, He Yadong ya ce Sin na matukar adawa da kakaba takunkumai daga bangare guda, da yiwa wasu sassa na nesa horo ba gaira ba dalili, ba tare da samun goyon bayan dokokin kasa da kasa, da amincewar kwamitin tsaron MDD ba. Don haka tabbas, kasar Sin za ta jajirce wajen kare halastattun hakkoki da moriyar kan ta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)