Naira ta ci gaba da samun tagomashi a kasuwar hada-hadar canji da aka gudanar inda Naira ake canja ta akan N1,500 kan kowacce dala Amurka maimakon a ranar Litinin da aka canjar kan N1,530 kowacce dala.
A kwanakin baya dai an samu tashin dalar a kasuwar canjin inda ake canja kowacce dala Amuraka daya kan N1,504, kuma ta sauka zuwa N1,502.5 a ƙarshen makon da ya gabata, kamar yadda bababban bankin Nijeria (CBN) ya bayyana cikin wani rahoto.
- CBN Zai Mayar Wa Da Masu Musayar Kudi Kudin Da Suka Biya Na Lasisi A 2025
- CBN Ya Sahale Wa Masu Musayar Kudade Sayen Dala 25,000 A Mako
‘Yan kasuwar bayan fage sun danganta alaƙar karyewar Naira da irin fasalin tsarin yadda ake samunta da kuma yadda ake bayar da ita daga babban bankin ƙasa (CBN)
Masu sharhi kan harkokin kuɗi a Cowry Asset Management suna tsammanin Naira za ta ci gaba da kasancewa kan yadda take a wannan makon, tare da ɗaukar matakan hana rugujewar ta a kasuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp