Darajar dan wasan gaban Real Madrid kuma dan asalin kasar Brazil Vinicius Junior na ci gaba da karuwa a kasuwar hada-hadar ‘yan wasan kwallon kafa, inda a cikin shekara daya ya ninka darajar sa fiye da sau daya.
A yanzu dai, dan wasan ne na uku a jerin ‘yan wasan da suka fi daraja a duniya, inda Kylian Mbappe ke kan gaba da darajar Yuro miliyan dari da 60 sai Erling Haaland da darajar Yuro miliyan 150 ya yin da Vinicius Junior ke da darajar Yur miliyan 120.
- Shugabannin Kasar Sin Sun Ajiye Furanni Domin Girmama Jaruman Kasar
- Csaba Korosi: Sin Ta Zamo Babbar Garkuwa Ga Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya Na MDD
A watan ktban shekarar 2021, darajar binicius ba ta wuce eur miliyan 50 ba, kasa da kudin da kungiyar Real Madrid ta say shi a shekarar 2018 amma a kakar da ta gabata dan wasan ya ta ka rawar gani a kungiyar sa ta Real Madrid, inda ya zura kwallaye 22 a dukkanin gasannin da ya buga ciki har da zura kwallo daya til a wasan karshe na gasar zakarun Turai, da kuma taimakawa wajen zura kwallaye 20.
Babu wani a cikin ‘yan wasa 10 da suka fi tsada a duniya da darajar sa ta karu da wuri tamkar binicius kamar yadda rahtan ya nuna sai dai hakan ya sam asali ne sakamakn irin kkarin da Real Madrid take yi a halin yanzu.