Rikici ya kara kamari a cikin jam’iyya mai mulki ta APC bayan korar daraktoci a sakateriyar jam’iyyar da ke Abuja, inda suka zargi shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu da handame biliyoyi wanda suka tura masa a asusun sirri ba tare da sanin kwamitin gudanarwa ba.
Daraktocin da aka kora sun zargi shugaban jam’iyyarda handame naira biliyan uku daga asusun banki na sirri.
A ranar 22 ga watan Afriluce, Adamu ya dakatar dadukkan rassan daraktoci da keshalkwatan jam’iyyar a Abuja bisa zarginsu da cin hanci da rashawa.
- Ba Mu Taba Ganin Ambaliyar Ruwa Mafi Muni A Nijeriya Kamar Ta Bana Ba – Gwamnati
- Sin Tana Maraba Da Kiran Taron Sulhu Tsakanin Al’ummomin Libya
Daraktocin sun hada da Elder Anietie Offong (Direktan walwala); Bartholomew I. Ugwoke (Daraktan bincike); Abubakar Suleiman (Daraktan kudade); Dakta Suleiman Abubakar (Daraktan gudanarwa); Salisu Na’inna Dambatta (Daraktan tallace-tallace) da kuma Dare Oketade (Daraktan lauyoyi).
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Adamu ya saura daraktocin. Tun lokacin da Adamu ya hau kan shugabancin jam’iyyar a ranar 1 ga watan Afrilu ya kafa kwamitin sauyi wanda tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Ali Saad Birnin Kudu ya ke jagoranta domin yin nazari kan shugabancin riko na Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da sauran matsalolin da suke addabar jam’iyya.
An dai bayyana cewa an kori daraktocin bias shawarar da kwamitin ya bayar.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya bayyana cewa duk irin kokarin da ya yi na jin ta bakin kwamitin gudanarwa amma lamarin ya ci tura. Sai dai a makon da ya gabata lokacin da yake fira da manema labarai, Adamu ya zargi daraktocin da cin hanci da rashawa.
Ya ce shugabancinsa ya gaji bashin naira biliyan 7.5 daga wurin kwamitin riko da Mai Mala Buni ya jagoranta.
Amma an musanta cewa bayanan da aka gabatar wajen korar daraktocin ciki har da shugaban sashin shari’a kwamitin bai bayar da shawara a sallame su ba tunda har yanzu ma’aikata ne na jam’iyya kuma dole a biya su hakkinsu.
Sun ce ikirarin da Adamu yake yi na cewa ya gaji bashin naira biliyan 7.5 daga jagoranci Buni karya ya shirga, wanda hasalima suka zargi shi da bude asusun banki na sirri ba tare da amincewar kwamitin gudanarwa ba, sannan ya bukaci su saka masa naira biliyan uku a ciki.
Lokacin da aka tuntubi Adamu a wayar salula ya musanta ikirarin daraktocin, inda ya bayyana cewa an adana kudaden ne ba wai don a kasha ba.
“An dai adana wadannan kudade ne ba wai domin a kashe su ba wanda su kuma suke kallon akasin haka. Ni ba ni da abokin fada, domin ni ina fada ne da hujja. Duk wadanda suke zargin an kasha wadannan kudade su fito karara su bayyana hujjojinsu.
“Duk abin da nake yi a matsayina na Abdullahi Adamu na kan shawarci kwamitin gudanarwa domin amincewa da dukkan wani mataki da aka bijiro da shi,” in ji shi.