Allah ya ce wa al’ummar Annabi su girmama shi (SAW), mutum ya girmama Manzon Allah domin ba kawai na ganin dama ba ne hakan, a’a, Allah ne ya ce ka girmama shi. Kila ma’anar girmama shi kuma, ana kira ne ga al’ummarsa su taimake shi. Kila kuma abin da ake nufi shi ne mutane su kai matuka wajen girmama shi, to ina wadanda idan suka ga an yi wani abu na girmama Manzon Allah (SAW) sai su rika cewa ana yin abin da Allah bai dora wa mutum ba, an ki barci, an barnata kudi kaza da kaza?
Yau dai ya kai matukar girmama Annabi (SAW) a ga mutum Dattijo ya hakura da barci, ya kashe kudinsa ya shafe dare cur a zaune saboda Manzon Allah (SAW). Ya fitar da kudinsa ya sayi dabba ko saniya ko rago ko wani abu ya ce ya yanka wa Manzon Allah (SAW), ai ya girmama ko? Ko ya dafa abinci, ko ya je Madina ya ziyarci Manzon Allah. Ba wai ya je Makka don yin Umura ko Aikin Hajji ba daga nan ya wuce, a’a, ya tashi musamman ya tafi Madina don ya ziyarci Manzon Allah (SAW), ka ga wannan ai ya girmama Manzon Allah saboda Allah ya ce mu kai matuka wajen girmama shi.
- Xi Ya Yi Jawabi Ga Taron COP14 Kan Kiyaye Filaye Masu Dausayi
- LEADERSHIP Ta Jinjina Wa Shehu Isma’ila Mai Diwani Kan Shafin Dausayin Musulunci
Amma yanzu wannan zai yi daidai da wanda zai ce ko an je Makka kar a ziyarci Manzon Allah? Ga shi nan za ka ga ana ta yin wa’azin hakan a Minna. Yanzu mai fadar wannan duk irin abin da zai fada na cewa shi ma Masoyin Manzon Allah (SAW) ai shi kansa ya san karya yake yi. Yanzu ko Babanka ne a Saudiyya, ka je Makka ka yi Hajji ko Umura amma ka ki zuwa ka ziyarce shi ka gaishe shi, me ka yi kenan? Ai ka zama dan baya. Baban naka ba zai ji dadi ba. Ballantana kuma a ce ba Babanka ba ne, Annabinka ne (SAW) wanda Allah ya ce mu kai matuka wajen girmama shi.
Wani sashen Malamai kuma (kila Abdullahi bin Abbas) ya karanta karatun da “wa yu abbizuhu”, maimakon “wa yu azziruhu), wato ayar tana nufin a girmama Manzon Allah, a kambama shi, a daukaka shi, gari gabadaya kowa ya yi kokari idan za a yi wani abu na girmama Manzon Allah (SAW) kowa ya yi iya karfinsa. Abin da ba a tabawa a gidanka rannan a fitar da shi a yi amfani da shi. Mun ga Malamanmu irin su Shehu Malam Murtala Gusau, ko cokali ya saya a Madinar Manzon Allah (SAW) to wanna n cokalin mai girma ne a wurinsa. Idan ka batar zai yi fada, ya ce idan ka batar da cokali dubu na gida ba komai, amma wancan a Madinar Manzon Allah (SAW) na sayo shi.
To yanzu kai dansa ko almajirinsa za ka yi wasa da Annabi? To amma ga wani can, ba wai cokali ko darduma da aka saya a garin Annabin yake girmamawa ba, a’a, Annabin ma gabadaya (SAW) ya ce ba sai ka ziyarce shi ba!
A karshen ayar kuma Allah ya ce a yi masa tasbihi safe da yamma, amma kuma sai ya hade abin da abubuwa na girmama Manzon Allah (SAW) don ya kara nuna mana girman Annabi. Wannan ishara ce da gargadi ga wadanda idan an girmama Manzon Allah (SAW) sai su ce an yi shirka, an kai Manzon Allah inda Allah bai kai shi ba (a uzu billahi), wani wuri ne wannan? A duk karatun duniya, ka dauko Alkur’ani kaf za ka ji irin matsayin da Allah ya kai Manzon Allah (SAW). Allah ya kai shi “kaba kausaini au adna”, ba malamin duniya tun daga Sahabbai zuwa yau da ya iya fassara “au adna”. To ka taba jin wanda ya kai wannan matsayin? Alkur’ani shi ne duk ya kakkai Manzon Allah (SAW) inda ake fada ba wani mutum ba.
Malam Dan Ada’u ya ce an tara wa Manzon Allah (SAW) ni’imomi a cikin wannan Sura (ta Fat’hi) mabanbanta, cewa Allah ya yi masa budi mabayyani, da cewa Allah ya amsa masa duk abin da ya roka (na cikin addininsa da al’ummarsa). Allah ya gafarta masa, ita gafarar nan tana daga sanarwar Allah yana son sa (duk mutumin da idan ya yi ma laifi ba ka ganin laifin, a kawo kararsa ya yi kaza da kaza; sai ka ce to sai me? ai ka san kana son sa kuma kowa zai shaida hakan).
Ita kuwa cika masa ni’ima da Allah ya yi, tana sanar da mu cewa Allah ya zabe shi kenan. Shiryarwarsa kuwa tana sanar da mu cewa Allah ya jibince shi, shi ya sa ya shiryar da shi. Gafara kuma ita ce kubutar da shi daga duk wani abu na laifi da aibi. Cikar ni’ima kuma ita ce an kai Manzon Allah daraja ta karshe har an kai shi matsayin “Wasila” da “Fadhila” (SAW). Shiriya ita ce kiransa (SAW) da aka yi ya je ya gana da Ubangijinsa, ba wani Annabi da ya samu wannan.
Sharifi Ja’afaru Dan Muhammadu (Sadik) RTA ya ce, yana daga cikar ni’ima da Allah ya yi wa Annabi Muhammadu (SAW) ya sanya shi a matsayin “Habibahu”, wato Babban Masoyinsa. Ya ishi girmamawa ga Manzon Allah da Allah ya rike shi Masoyi. Allah ya rantse da rayuwarsa (mun yi wannan karatun a baya). Allah ya soke shari’o’in Annabawa duka da Shari’ar Manzon Allah (SAW). Allah ya yi Mi’iraji da shi, wato ya hawar da shi zuwa bigire madaukaki da ba wani abin Halitta Dan Adam ko Mala’ika da ya taba zuwa. Babu wata halitta da ta taba zuwa nan. Allah ya kiyaye shi a cikin tafiyar (ta Mi’iraji), har ya zamo idonsa bai karkace ba kuma bai yi shan zara ba. Allah ya aiko shi zuwa jar fata da bakar fata. Allah ya halatta masa da al’ummarsa ganimomin yaki.
Allah ya sanya shi mai yin ceto ranar tashin kiyama kumwanda za a karbi ceton nasa. Allah ya sanya shi a matsayin shugaban ‘ya’yan Adam kaf. Allah ya hada ambatonsa da ambaton Allah. Allah ya sanya yardar Manzon Allah ta zama yardar Allah ce. Allah ya sanya shi a matsayin dayan rukunin Tauhidi, wato in dai ka ce “La ila ha illal lahu” ba ka ce “Muhammadur rasulullahi” ba, Musuluncinka bai tabbata ba. Kafiri idan ya zo shiga Musulunci aka ce ya fadi “La ila ha illal lahu…” ya fada, aka zo “Muhammadur rasulullah” sai ya ce a’a, ai cewa aka yi a kadaita Allah don haka ba sai ya fad aba, idan ya yi haka, shin ya musulunta? Ai Musuluncinsa bai inganta ba.
Allah Tabaraka wa Ta’ala ya kara cewa “Lallai wadanda suka yi caffar hannu da kai, kadai dai, da Ubangiji suka yi, kuma Hannun Allah (yadda ya dace da shi) ne kan hannunsu…”
Wannan kissa ce da kowa ya sani, kissar Hudaibiyya ce (Bai’atur Ridwani), wacce sahabbai suka yi wa Annabi alkawarin shiga Makkah ko da za su rasa rayukansu da dukiyoyinsu.
Wani karin misalin kuma shi ne inda Allah yake cewa, “Falam Taktuluhum, walakinnallah Katalahum” Ya rasulullahi ba kai ka kashe su ba, Allah ne ya kashe su.
A wani wurin kuma Allah ya ce, “Wa ma ramaita, iz ramaita walakinnallaha rama” ba kai ka yi jifa ba yayin da ka yi jifa, Allah ne ya yi. Kissa ce ta ranar yakin Badr, yayin da Annabi ya debi kasa ya watsa wa rundunar kafirai har sai da ta shiga idon mutum dubu (1000), haka kuma a yakin Hunaini, Manzon Allah (SAW) ya sake diban kasa ya watsa wa rundunar kafirai har sai da ta shige idon mutum dubu talatin (30,000). Amma wadannan Ayoyi sun zo a babin Hakika, don kowanne musulmi yana da Imanin cewa Allah ne ke yin Komai.
Allah shi ne Mahaliccin jifan da mai jifan, sai dai wanda ya yi jifan Annabi ne kuma Kalifan Allah ne – Dan Adam amma ba kamar sauran ‘yan Adam ba.
Yana daga cikin girmamawar da Allah ya yi wa Annabi daga kissar Isra’i da yake cewa “Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa, daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Kudus Wanda Allah ya albarkaci kewayensa, don mu nuna masa wani abu daga cikin ayoyin kanmu, kuma Lallai Allah mai ji ne kuma mai gani ne (Ko kuma shi ma Annabi Allah ya karfafe shi da jin da ganin)”.
Wasu suna tambaya cewa, me ya sa Allah ya ce ” Don mu nuna masa wani abu daga cikin ayoyin kanmu”, amma kuma ya ce ma Annabi Ibrahim “Mun nuna masa mulkinmu na sama da na kasa”
Sai Shehu Ibrahim Kaulaha (RA) ya bada amsa da cewa “Shi Annabi Ibrahim mulkin sama da kasa ya gani, shi kuwa Annabi don mu nuna masa wani abu daga cikin ayoyinmu, ma’ana Zatinmu. Shi ya sa Allah ya ce wani abu daga cikin ayoyinmu. Ayoyin Allah babu wanda ya isa ya san su duka, sai dai wani dan abu daga ciki. Wani dan abu daga cikin sanin Zatin Allah, ya fi duk mulkin sama da kasa.
Akwai kuma wani karin girmamawa da Allah ya yi wa Annabinsa a Suratun Najmi ‘Wan najmi’.
Ita Suratu Isra’i ta yi bayanin hawa sama, ita kuma Suratu Najmi ta yi bayanin yadda aka yi a bayan hawan.