A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bikin bude taron wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniyar Ramsar kan yankuna masu dausayi ko COP14 a takaice.
Ana gudanar da taron ne daga yau Asabar 5 zuwa 13 ga watan Nuwanba, a birnin Wuhan na lardin Hubei dake yammacin tsakiyar kasar Sin, a matsayin wurin dake karbar bakuncin taron, da kuma makamancin taron dake gudana a Geneva na kasar Swizerland, dukkansu a zahiri da kuma ta kafar intanet. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Talla