Yayin da Allah ya yi wa Annabi (SAW) kashafi sai ya nuna ma sa ikonsa da sarautarsa masu ban mamaki wadda babu wata fassara da za ta iya fada, hankali ba zai iya kamawa ba. Don haka ne Allah ya dunkle maganar baki daya ya yi nuni da ita, ya yi jirwaye-mai-kaman-wanka a bisa nuna girman Manzon Allah (SAW) inda ya ce “Sai Allah ya yi wa bawansa wahayin abin da ya yi ma sa”. Mene ne wannan?, Allah ne mafi sani. Wannan nau’i na magana cewa ‘an yi wa mutum abin da aka yi ma sa’ yana nufin an yi wa mutum abu mai yawa, idan alheri ne za a gan shi mai yawa, haka nan idan kishiyarsa ne. Malamai masu ilimin balaga suna cewa irin wannan maganar, ita ta fi kai matuka wajen takaita magana. A ayar da Allah ya yi rantsuwa ya ce Manzon Allah “ya ga ayoyin Ubangijinsa masu girma”, tunaninmu ya takaita wurin gane ko fahimtar abin da ya gani (in dai ba shari’a ce ta fada mana ba). Hankulanmu sun dimauta su iya gane meye wadannan ayoyin na Allah manya da ya ce Manzon Allah (SAW) ya gani.
Ma’anar kashafi da muka bayyana a baya shi ne, misali idan mutane suna zaune a wuri daya za su ga kawunansu da abin da ke kewaye da su amma kuma watakila akwai sauran wasu halittun Allah da idanuwansu ba za su iya gani ba (kamar Aljannu ko Mala’iku), to shi kuwa wani bawan Allah yana nan Allah ya yaye masa zai iya ganin abin da mutanen nan ba su iya gani da idanuwansu. Wannan idon namu ba komai yake iya gani ba. Sai dai kuma, abubuwan da ake iya gani kala-kala ne. Yanzu misali idan wani ya zo ya ce ya ga Annabi (SAW) to ba za a karyata shi ko gaskata shi ba tukuna, sai a dubi halinshi, idan mutumin kirki ne mai ibada; mai tsarki sai a gaskata shi amma in mutumin banza ne sai a karyata shi, ya je can shi da abin da ya gani. Saboda tsarkake Annabi sai a karyata shi (mutumi mai mafarkin). Lallai Allah yana budi ga wasu bayinsa su ga abubuwan da ba kowa ke gani ba.
- Falalar Ziyarar Kabarin Annabi SAW (2)
- Tsarin ‘Yancin Kasuwanci A Afirka: Nijeriya Za Ta Amfana Da Dala Biliyan 50
Malam Alkadiy Iyad ya ce wadannan ayoyi na “Wannajmi” guda 18 sun tattare sanarwar Allah kan yadda ya tsarkake komai na Annabi (SAW). Allah ya sanar da mu a cikin wadannan ayoyin cewa ya tsarkake Manzon Allah baki daya. Sannan ya rika bin gaba-gaba na Annabi yana magana a kai.
Kuma Allah ya tsare Manzon Allah (SAW) daga aibi a wannan tafiya da aka yi. Duk abin da ya fadi a game da tafiyar gaskiya ya fada. Allah ya tsarkake zuciyarsa (da take rike abin da ido ya gani), ya tsarkake harshensa da dukkan gabbansa. Wurin tsarkake zuciya Allah ya ce zuciyar Manzon Allah (SAW) ba ta karyata abin da ya gani ba, ma’ana ya san me ya gani. Da aka tambaye shi (SAW), ya ce “Na ga Ubangijina”, “Na ga Al’arshi” ya lissafa shimfidunta iri kaza, “Na ga Kursiyyu, na ga Rafrafu, na ga Aljanna, na ga wuta”, duk Hadisan Isra’i sun zo da bayanan wadannan. Allah ya tsarkake harshensa (SAW) da fadarsa cewa Manzon Allah ba ya furuci a bisa son rai sai an ma sa wahayi. Allah ya tsarkake idonsa da ya ga ayoyin da su a inda Allah ya ce “Idonsa bai kauce ba, kuma bai tsallake iyaka ba”. Yanzu misali muna ganin rana amma ba mu san ta ba. Idan mun iya rutsa idonmu muka kalle ta wani dan kwallo ne za mu gani da kore-kore a cikinta, aba ce ta wuta amma idonmu yana nuna mana kore ne a ciki. Wuta ce da ta ninninka ta duniya. Malaman sanin falaki (physics) sun ce girman rana ya ninninka duniya sau adadi da yawa amma sai ga shi idonmu yana nuna mana girmanta kamar kwallon kafa. Idan ka je gaban abin da ya ninka duniya yaushe za ka ga farkonsa ko ka ga karshensa? Don haka har yau ba mu iya ganin rana ba. Amma idon Manzon Allah (SAW) ya riski abin da ake so ya gani. Akwai wani karatu mai zurfi a wajen.
Allah Tabaraka wata’ala da hikimarsa ya fada mana wani karatu. Manzon Allah (SAW) ya ce Allah ya yi wa Aljanna fenti da abubuwan da muke ki (wahala, yawan ibada da sauran su), ka ga ba za mu yi kusa da ita ba kenan in ba don falalar Allah ba. Manzon Allah ya kuma ce Allah ya yi wa wuta fenti da abubuwan da muke so (barna, bata abubuwa), a nan sai mai hankali ne zai fahimci ya kamata ya kutsa wa wannan abubuwan da rai ba ya so don ya shiga Aljanna, ko ya hakura da wannan dadin na wajen wuta don ya kauce wa azabar Allah.
Allah Tabaraka wata’ala shi ya kira Annabi (SAW) don ya yi Isra’i da shi ya nuna ma sa ayoyinsa manya. Kuma cikin Kudura ta Allah da Ibtila’i (Allah ya fi jarraba manya dama), maimakon Annabi (SAW) ya shige zuwa fadar Allah; sai ya ci karo da wata bishiya da aka yi wa ado (Manzon Allah ya ce ‘ya’yanta kamar Tulunan Hajaru, ganyenta kamar Kunnen Giwa dukkansu an musu ado da gwalagwalai) amma Annabi (SAW) kallonta ma bai yi ba saboda abin da yake gabansa (na ganin Alah) ya fi duk wannan. Sai Allah ya yabe shi da cewa “idonsa bai karkata ga duk wannan ba”. Haka nan ma a hanya, duniya ta kira shi amma Annabi duk bai kula da su ba. Allah ya kiyaye ya tsarkake ganinsa (SAW).
A cikin wasu ayoyin kuma dai da Allah ya yi kirari ga Annabi (SAW) na cikin Suratut Tak’wiri, Allah (SWT) yana cewa “ina rantsuwa da taurari masu nokewa (idan sun kai karshen buruji sai su koma farko, su ne guda biyar: Zuhal, Mushtariy, Mubriku, Zahratu, Kudaritu. Su ma Turawa masu falaki suna da sunayensu: Mars, Jupiter, Neptune da sauran su)”. Su ne wadannan taurarin masu tafiya suna faduwa. Allah ya kuma ce “Na yi rantsuwa da dare idan duhunsa ya fuskanto”. “Na yi rantsuwa da asuba yayin da ta numfasa”. Idan dare ya take sai ka ji komai ya yi cik amma da Alfijir ya keto sai ka ji kamar an saki iska, hayaniyar abubuwa sun cika ko ina. Iska mai dadi da ake kira ‘Saba’ ta rika tasowa, tsuntsaye su fara kuka. Don haka fitowar Alfijir kamar numfashin dare ne. Shi ya sa Allah ya ce ya rantse da asuba idan ta nunfasa. Jawabin wadannan rantse-rantse shi ne: wallahi “wannan Kur’anin maganar annabi ne mai girma a wajen Allah (ai mai girma wajen wanda ya aiko shi)”. Ba wai maganar Manzon Allah ake nufi ba, ana nufin wanda aka aiko ya kawo Kur’anin ga al’umma (Manzon Allah SAW), mai girma ne a wajen Allah. A nan ko mutane ba su ga girman Annabi (SAW) ba, to ya isar ma sa girman da yake da shi a wurin Allah. Kuma shi Annabi, “Ma’abocin karfi ne a bisa isar da abin da aka dora ma sa na Manzanci”. Har a ranar Hajjin bankwana da ayar da ta cika shari’a (Shikashikan Musulunci) ta sauka, Manzon Allah ya ce wa al’umma “idan na koma wurin Ubangiji ya tambaye ku, me za ku ce? Shin na isar?” Suka ce “eh mun shaida ka isar”. Sai ya ce “Ya Allah ka shaida su da kansu sun shaida na isar musu”. Manzon Allah ya fadi haka har sau uku (SAW).
A cikin surar, Allah ya ci gaba da bayyana Manzon Allah (SAW) a matsayin “Mai tabbatacciyar daraja (matsayi) ne daga Ubangijinsa”. Ma’ana yana da daukakar daraja a wurin Allah. “Abin bi ne (a sama) sannan amintacce ne (wurin isar da wahyi)”. Manzon Allah ya isar da Manzancinsa, bai kara ba; bai rage ba (SAW).
Malam Aliyu Dan Isah (Malamin Tafsiri, Nahwu, Lugga da sauran su) mutumin Bagdad, Almajirin Ibn Duraid, ya ce Ma’aikin da ake nufi a wannan wurin (ayar) Annabi Muhammadu ne (SAW). Dukkan wadannan siffofi a bisa fassarar Malam Aliyu duk na Manzon Allah ne (SAW).
Wasu Malamai kuma suka ce ayoyin suna magana ne a kan Mala’ika Jibrilu (AS). Idan aka tafi a wannan fassarar, to karfin da sauran siffofin sai su koma wurin Jibrilu (AS).
Allah Tabaraka wata’ala ya ci gaba da cewa “Hakika (Manzon Allah) ya gan shi (Mala’ika Jibrilu) a sasannin mahudar rana mabayyani”. Sai dai lamirin da aka yi amfani da shi a cikin ayar, watakila an ce fassararsa “ya ga Ubangijinsa” ne. Sayyidina Abdullahi bin Abbas da wasu daga cikin Sahabbai (RA) suka ce Manzon Allah ya ga Ubangijinsa ne. Wadanda suka kafa hujja da maganar Sayyada Aisha (RA) kuma suka ce “ya ga Jibrilu” ne. Sayyada da ta ce Manzon Allah Jibrilu ya gani, amma ba cewa ta yi Manzon Allah ne ya fada ma ta ba. Ijtihadi ta yi ta fassarar ayar “Ido bai riskar ganin Allah…”, idan Sahabi ya kawo abu, sai aka samu maganar Annabi (SAW) a kai, toh shikenan sai a karbi na Annabin. Akwai Hadisin da Manzon Allah (SAW) ya ce “na ga Ubangijina”, kun ga yanzu wannan ya warkar. Idan bai inganta ba (Hadisin), to maganar Abdullahi bin Abbas a kan Manzon Allah ya ga Ubangijinsa ta inganta. Idan aka samu Sahabbai biyu, wannan ya ce akwai; wannan ya ce babu, to sai a dora na wanda ya ce akwai a kan na wanda ya ce babu. Abdullahi bin Abbas ya tabbatar da cewa Manzon Allah (SAW) ya ga Ubangijinsa. Ya ce ai abubuwa ne guda uku. Annabi Ibrahim (AS) an bashi Badadantaka, Annabi Musa (AS) an bashi –jin- maganar Allah, shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) sai aka hada ma sa jin maganar da gani. Hadisai ne da yawa a wurin.