A wani lamari na sauya sabon salo dangane da rikicin sarautar Kano, Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sake maido da masarautu uku daga cikin hudu da ya rushe.
A rana daya Majalisar Dokokin Kano ta gabatar da kudirin samar da dokar kirkirar masauratun masu daraja ta biyu, aka yi mata karatun da ya kamata, aka zartar da dokar, sannan aka kai wa gwamna kuma ya rattaba mata hannu da yammacin ranar Talata.
Bayan gwamna ya rattaba wa dokar hannu, nan take kuma ya amince da nadin sabbin sarakuna masu daraja ta biyu da suka hada da masarautun Gaya, Rano da Karaye. Gwamnan ya nada Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin nadinsa shi ne Hakimin Rogo.
Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin nadinsa shi ne Hakimin Bunkure, sannan kuma Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda shi ne tsohon Sarkin Gaya.
Wannan mataki na gwamnatin Jihar Kano ya zama wani sabon salo, domin a lokacin da ake tsaka da ce-ce-ku-ce a gaban kotuna daban-daban kan rikicin masarautun na Kano, an ji yadda wasu kotunan suka tabbatar da dakatar da Sarki Muhammadu Sanusi II da kotunan gwamnatin tarraya suka zartar tare da cin tarar gwamnatin Kano na naira miliyon 10. Haka itama wata kotu a Jihar Kano karkashin Mai Shari’a Amina ta tabbatar da haramta wa Sarki Aminu Ado da sauran sarakuna uku ayyana kansu a matsayin sarakuna.
Ana tsaka da wannan danbarwa ne sai kuma a ranar Talata da ta gabta, bayan dawowar majalisar dokokin Jihar Kano daga hutun sama da kwanaki 40, inda majalisar ta fara da wani kudiri da aka bukaci samar da dokar kirkirar masauratu masu daraja ta biyu, aka kuma amince tare da mika kunshin dokar, inda gwamnan ya rattaba mata hannu a lokaci guda kuma ya amince tare da nada sabbin sarakuna uku masu daraja ta biyu wadda a wannan rana aka mika masu takardun kama aiki
Wannan sabon mataki na gwamnatin Kano kan sarkakkiyar da ta dabaibaye masarautun Kano na nuni da cewa ga dukkan alamu sarakuna biyu uwa daya uba daya, Alhaji Aminu Ado Bayero da dan’uwansa, Alhaji Nasiru Ado Bayero na alamta cewar an tsame su daga cikin jerin sarakunan da ake magana akansu, musamman Masarautar Bichi wadda babu ita baki daya daga cikin sabuwar dokar.
Shi dai tsohon sarkin Gaya mai daraja ta daya, wanda yanzu kuma aka sake mayar da shi a matsayin sarkin na Gaya, amma a wannan karon mai daraja ta biyu, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya rabauta da sake darewa kan karagar sarautar ta Gaya, sakamakon matakin da ya dauka tun a lokacin da Gwamnatin Abba ta sanar da sauke su, inda shi kadai ne wanda ya fito fili ya karbi wancan kaddarar, kila hakan tasa gwamna ya sake aminta da nadisa a matsayin sabon Sarkin Gaya a wani salo na saka masa bisa karbar hukumcin da gwamnati ta yanke a kansu tun da farko.
Sai dai kuma wadannan sabbin sarakuna masu daraja ta biyu an sare masu fika-fikai, domin sarkin Gaya na da iko ne kawai da kananan hukumomi uku, wanda suka hada da Gaya, Ajingi da Albasu, shi kuma Sarkin Rano na da kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, yayin da sarkin Karaye ke da iko da kananan hukumomin Karaye da Rogo, shi kuma Sarki Muhammadu Sanusi II sarki mai daraja ta daya kamar yadda sabuwar sokar ta nuna yana da kananan hukumomi 36 da suke karkashin ikonsa.