Bayan da kasar Ibory Coast ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2023 wanda daman ita ce ta karbi bakunci, ana ganin cewa gasar ta wannan karo itace mafi kayatarwa a tarihi.
Akwai abubuwan ban mamaki daki-daki a labarin hanyar da Ibory Coast ta bi kamar wani abu na almara da ta kai ta ga lashe kofin bana duba da gazawar da kasar ta nuna a wasannin rukuni. Dan wasa Sebastien Haller, wanda ya koma buga wasa bayan watanni 13 da aka yi masa aiki kan ciwon daji, shi ne ya ci kwallon da ya kai Ibory Coast wasan karshe a karawar da suka yi da DR Congo.
- Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu-Maryam Labarina
- Tsadar Rayuwa: Sheikh Muhajjadina Ya Nemi Gwamnati Ta Gaggauta Daukar Mataki
Sannan dan wasan Borussia Dortmund shi ne ya zura kwallo na biyu a ragar Nijeriya da ya kai mai masaukin baki ta lashe AFCON na 2023 haka kuma nasara ce mai girma ga kociyan rikon kwarya, wanda ya ja ragamar wasa hudu, kuma manya a fannin tarihin horar da kwallon kafa.
A hirarsa da manema labarai, kociyan tawagar Ibory Coast Emerse Far ya ce ”Wani abu ne fiye da na almara bayan farke kwallon da Nijeriya ta ci Ibory Coast, sannan ta kara ta biyu ta lashe kofin a wasan karshe.
Ya ci gaba da cewa ”Idan na tuna dukkan halin da muka tsinci kanmu, mun kasance ‘yan sa’a mun jure da kuma fuskantar kalubalen da muka fuskanta har zuwa wasan karshe”
Tawagar Ibory Coast ta kori kociyanta Jean Louis Gaset, bayan da kadan ya rage a yi waje da ita daga karawar rukuni – sannan ta fitar da mai rike da kofin Senegal a bugun fenariti a karawar zagaye na biyu.
Sannan kasar ta ci kwallo dab da za a tashi daga fafatawar dab da na kusa da na karshe a minti na 122, sai dai yanzu abin da ake jira shi ne ko kociyan mai shekara 40 zai karbi jan ragamar tawagar Ibory Coast?, batun da bai yadda ya tattauna ba tun kan wasan karshe.
Mai masaukin baki
Gwamnatin Ibory Coast ta kashe sama da Dala biliyan daya wajen karbar bakuncin wasannin ciki har da gida sabbin filin wasa hudu da yi wa biyu gyara an kuma yi gyara ko sabon gini a filayen sauka da tashin jirgin sama da hanyoyi da otel a manyan birane biyar a Ibory Coast da ya hada da Abidjan da Bouake da Korhogo da San Pedro da kuma Yamoussoukro.
An yi murna da yawa a kasar da ta dauki bakuncin wasannin, inda riguna masu launin ruwan goro a ko’ina a fadin kasar da kuma suke halartar filaye da yake cika makil, wadanda da farko ba a samu ‘yan kallo da yawa ba.
An samu ci gaban sufuri da aka samu karin kudin shiga a yawan bude ido, yayin da shugaban kasar Alassane Ouattara ya shiga cikin ‘yan wasa domin murnar lashe AFCON a kasar kuma karo na uku jimilla.
Daga nan ne dubban magoya baya suka kashe kwarkwatar ido a lokacin da tawagar ta zagaya Birnin Abidjan da kofin a budaddiyyar mota ranar Litinin. Gasar AFCON ta bana an yi abin ban mamaki, inda Ekuatorial Guinea ta caskara mai masaukin baki, Ibory Coast, kuma ta ja ragamar rukunin farko a rukuni na daya mai dauke da Nijeriya.
Haka itama Cape Berde ta yi ta daya a rukuninta duk da fitattun kasashen da ta kara da su, sai kasashen Namibia da Angola suna daga hudu masu rauni daga kasashe 24 da suka je Ibory Coast, amma sun kai zagaye na biyu, yayin da Mauritania ta ci wasan farko a AFCON a tarihi, sannan Afirka ta Kudu ta dagula lissafin Morocco a hanyarta ta zuwa ‘yan hudun karshe.
Gasar AFCON ta 2023 an ci kwallo 119 wanda hakan yake nufin kenan ana zura kwallo 2.29 a raga a kowanne wasa. Gasar da ka zazzaga kwallaye a raga ita ce da a ci 2.38 a duk karawa a shekarar 2012.
Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka CAF ta ce sama da mutum biliyan biyu ne suka kalli gasar a talabijin – kenan wasannin gasar da aka fi kallo a tarihi kenan – inda kasashe 173 suka kalli karawar karshe.
An ci kwallaye a dab da za a tashi daga wasa, inda rukuni na biyu aka fi samun hakan musamman a minti na 89, fiye da irin abin da ya faru a shekarar 2021, sannan kwallo hudu da mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, Ronwen Williams ya tare ya kara fito da rawar da masu tsaron raga suka taka a babbar gasar ta Afirka ta 2023.
William Troost-Ekong
Duk da cewa Nijeriya ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun mai masaukin baki, kyaftin din tawagar Nijeriya Williams Troost-Ekong shi ne wanda aka zaba gwarzon gasar baki daya. Ekong, mai shekara 30 a duniya ya zura kwallaye uku a gasar kuma shi ne ya buga kowanne wasa tun daga farko har karshe.
Shi ne jagoran ‘yan wasan baya na Super Eagles inda a gasar Nijeriya ta buga wasanni hudu ba tare da an zura mata kwallo a raga ba, kuma shi ne dan wasa na farko a Nijeriya a tarihi da ya zura kwallo uku a raga a wasa daya tun dan wasa Ali Al-Beshari dan kasar Libya da ya kafa wannan tarihin a shekarar 1982.
Na’urar VAR da alkalan wasa
Abu ne mai wahala ka ga koci ya yaba da hukuncin da na’urar fasahar ta zarar musamman da bai yi wa kungiyarsa dadi ba – amma kociyan Super Eagles, Jose Peseiro ya yi jinjina a lokacin wasan dab da karshe da Afirka ta Kudu.
Super Eagles na ganin ta ci kwallo ta biyu a minti na 85 ta hannun Bictor Osimhen, amma sai aka soke kwallon sannan aka bai wa Afirka ta Kudu fenariti, maimakon bugun laifin kafin Nijeriya ta ci kwallo ta biyun.
An yi amfani da na’urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci BAR kamar yadda ya kamata da hukunce-hukunce da suka da ce ta kuma taka rawar gani a gabaki dayan wasannin.
Kasashen da suka kasa taka rawa –
Ghana
An yi waje da Ghana, wadda ta lashe kofin sau hudu tun daga karawar cikin rukuni, bayan da ta bai wa Cape Berde sadakar kwallo a minti na karshe kuma Ghana ta fita daga gasar tun a cikin rukuni.
Bayan ficewar Ghana daga gasar ne kuma kociyan tawagar, Chris Hughton ya rasa aikinsa bayan da hukumar kwallon kafar kasar ta kore shi daga aiki sakamakon rashin tabuka abin kirki domin rabon da Ghana ta buga gasa mafi muni a tarihin gasar AFCON tun a shekarar 1982.
Wani tarihin kuma shi ne, tawaga daga Arewacin Afirka ta kai wasan karshe daga gasa uku baya, saboda abin mamaki ne da ba a samu daya daga ciki ba da ta kai wasan karshe a bana.
Hudu daga cikin wadanda suka halarci wasannin bana suna daga biyar da ke matakin farko a kan gaba a iya kwallo cikin tawaga 24 da suka je Ibory Coast sai dai tuni aka yi waje da Algeria, bayan da Mauritania ta doke ta da wasan da Tunisia ta yi rashin nasara a hannun Namibia, wadda take da tazarar gurbi 85 tsakaninta da Tunisia.
A wasan zagaye na biyu a gasar, Afirka ta Kudu ta fitar da Morocco daga wasannin, wadda ta kai zagayen dab da karshe a gasar kofin duniya a Katar, yayain da Masar mai kofin guda bakwai ta yi ban kwana da gasar sakamakon da DR Congo ta yi nasara a bugun fenariti.
Kasar Morocco ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin Afirka da za ta gudanar a shekarar 2025, wadda za ta yi fatan lashe kofin a karon farko tun bayan wanda ta dauka a 1976.
Mohamed Salah
Bayan da Masar ta yi ta biyu a shekarar 2017 da kuma a 2021, kyaftin din tawagar ya yi hira da ‘yan jarida kan yadda yake fatan kawo karshe shekara 14 ba tare da ya lashe kofin ba.
Dan wasan Liberpool shi ne ya farke kwallon da Mozambikue ta ci Masar da suka tashi canjaras, amma an canja shi a zagaye na biyu a wasa da Ghana, bayan raunin da ya ji kuma ya koma Ingila domin likitocin kungiyar Liberpool su ci gaba da duba lafiyarsa kuma tuni har ya warke ya fara buga wasa.
Masu horarwa
Mai koyarwa Chris Hughton shi ne na farko da aka fara kora a AFCON a shekarar 2023, daga baya shida daga cikin koci 24 suka bar aiki ko dai an kore su ko kuma suka yi ritaya.
Cikin wadanda aka kora sun hada da na Algeria, Djamel Belmadi da na Tunisia, Jalel Kadri da na Masar, Rui Bitoria sakamakon kasa taka rawar gani, shi kuwa Tom Saintfiet ajiye aikin ya yi, bayan da aka fitar da Gambia, yayin da Guinea-Bissau da Burkina Faso suka yanke shawarar ba za su tsawaita kwantiragin Baciro Cande da kuma Hubert Belud.
Shi kuwa Adel Amrouche an dakatar da shi ne bayan da kociyan tawagar Tanzania aka dakatar da shi wasa takwas a hukuncin da Caf ta dauka.