• English
  • Business News
Saturday, June 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah S.A.W (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani and Sulaiman
18 hours ago
in Dausayin Musulunci
0
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Masu karatu da fatan an yi sallah lafiya. Allah ya maimaita mana na badi cikin koshin lafiya da wadata Albarkar Annabi (SAW). Allah ya dawo mana da mahajjatanmu gida lafiya.

Za mu dan yi matashi kadan daga darasinmu na makon da ya gabata daga nan sai mu dora.

  • Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka
  • Cikakken Jerin Sunaye: Tinubu Ya Karrama ‘Yan Nijeriya 102 Don Bukin Ranar Dimokuradiyya Ta 2025

Hadisin ya koyar da cewa an so ga Alhaji idan zai fara Dawafi ya fara da sumbantar Hajarul As’wad. Sannan zai yi kewaye uku na farkon Dawafinsa da sassarfa (ba gudu ba kuma ba tafiya ba, tsaka-tsaki). Sauran kewaye hudun kuma zai yi da tafiya.

Wani abu da Hadisin bai kawo ba a nan (amma kuma akwai shi a shari’a) shi ne, idan namiji zai fara Dawafi ya shigo da mayafinsa ta karkashin hammatarsa ta dama, ya zama damtsensa yana waje, sai ya yafo shi ta kafadarsa ta hagu. Ma’ana damtsensa na dama yana waje, na hagu tare da hannunsa kuma suna cikin mayafin.

Bayan kammala Dawafi, sai mutum ya yi Sallar Nafila raka’a biyu a bayan Makamu Ibrahim (a yanzu an lullube wurin da Kwalbar Zinare), raka’a ta farko a karanta Fatiha da Kulya (Suratul Kafiruun), raka’a ta biyu Fatiha da Kulhuwallahu (Suratul Ikhlas).

Labarai Masu Nasaba

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)

Hadisin Aikin Hajjin Annabi (SAW) ya koyar da cewa sumbantar Hajrul As’wad yayin da aka shiga Ka’aba da kuma sake sumbantarsa yayin fita sunnah ce, amma idan mutum bai samu iko ba; ya yi sumbar ta hanyar nuni da hannu.

Hadisin ya kuma nuna mutum zai je ya yi Safa da Marwa. Zai fara da Safa kamar yadda Annabi (SAW) ya yi. Mutum zai hau kan Safa har sai ya ga dutsen, da yake sun rufe shi da gilashi sai a matsa kusa da shi. Idan ya yiwu sai a kalli Ka’aba a ambaci Allah, sannan a yi addu’a. Za a maimaita haka sau uku.

Idan mutum ya iya, ya ce “Subhanallahi wal-Hamdulillah wa La’ilaha’illallahu wal-Lahu akbar. La’ilaha’illallahu wahdahu lashariyka lahu sadaka wa’adahu wa nasara abdahu wa hadamal ahzhaba wahdahu”. Idan mutum bai iya ba, ya yi ta fadin La’ilaha’illallah. Sai ya yi addu’a.

Daga nan ya gangaro zuwa Marwa, a kan hanyarsa zai ga wani wuri da aka sanya koriyar fitila (tsakiyar Safa da Marwa), ana so ya yi sassarfa a wurin. Zai rika yin sassarfar a duk lokacin da ya zo wurin har ya kammala Sa’ayi, ba kamar sassarfar Dawafi da ake yi a kewaye uku ba kawai. Idan mutum ya hau Marwa, a can ma zai yi Zikiri ya yi addu’a.

Hadisin ya nuna cewa idan mutum ya kare Sa’ayi a kan Marwa, to ya kammala Umurarsa sai kawai ya yi aski amma ga mai Tamattu’i.

Bayan ya koma gida zai cigaba da harkokinsa na halas ciki har da kwanciya da iyali wadda aka haramta masa lokacin da ya yi harama har sai zuwa ranar Tarwiyya da za a yi niyyar Hajji.

Wani darasin Hadisin kuma shi ne, duk wanda ya warware haraminsa bayan ya kammala Umura, zai sake yin niyyar Hajji tare da fita zuwa garin Mina. Haka nan shi ma wanda bai warware ba (mai Hajjin Kirani) zai fita zuwa Mina. Sannan yana daga sunna mutum ya yi sallolin farilla guda biyar a can Mina (Azahar, La’asar, Magriba, Isha’i da Subahi). Kuma mutum zai kwana a Mina (daren ranar Arfa).

Haka nan sunna ce mutum kar ya fita zuwa Arfa har sai rana ta fito, kuma kar ya shiga Arfa sai bayan rana ta yi zawali (lokacin Azahar). Idan mutum yana da kokari, bayan an shiga Arfa sai ya tafi can Masallacin Namira ya saurari huduba; a yi Sallolin Azahar da La’asar da shi lokaci daya. Bayan kammala sallolin sai ya dawo Arfa (hukumomin can sun sanya alamomin da ke nuna kan iyakokin Arfa).

Yana daga sunna Liman ya yi huduba kafin gabatar da sallolin nan (Azahar da La’asar). Wannan ita ce huduba ta biyu, ta farkon ita ce wacce Annabi (SAW) ya yi a rana ta bakwai ga Zhul-Hijja. Akwai kuma huduba ta uku da Liman yake yi ranar Sallah, sai kuma ta hudu a ranar tafiya ta farko (kwana biyu bayan sallah).

Hadisin ya kuma koyar da mu cewa bayan mutum ya dawo daga sallolin, zai dawo cikin Arfa ya tsaya a kan abin hawansa (idan yana da hali), don haka Annabi (SAW) ya yi. Idan bai samu ba, sai ya zauna ya cigaba da yin Zikiri da addu’o’i har rana ta fadi. Idan mutum ya samu hali ya je wurin da Annabi (SAW) ya tsaya, idan bai samu shi kenan, ko ina (inda aka shata) Arfa ne. Ana so a fuskanci Alkibla yayin tsayuwar ana addu’a. Babu laifi a je a ci abinci ko a dan yawata saboda gajiya duk dai a cikin kewayen Arfar.

Annabi (SAW) ya ce fiyayyen abin da ake karantawa ranar Arfa shi ne: “La’ila’ha’illallahu wahdahu lashariyka lahu lahul mulku wa lahul hamdu yuhyi wa yumiytu wa hul hayyu layamuutu biyadihil khair wa huwa ala kulli shai’in kadiyr”, guda 100.

Bayan an taso daga Arfa sai a nufi Muzdalifa cikin natsuwa ban da gaggawa. Annabi (SAW) ya rika jan akalar abar hawansa har kanta yana taba sirdi domin tafiya a hankali zuwa Muzdalifa. Hadisin ya kuma nuna mutum ya rika horon mutane da natsuwa a yayin komawa Muzdalifa. Da farko shi ya tabbatar da ya natsu, kana sai ya hori wasu da yin hakan.

Idan mutum ya isa Muzdalifa sai ya sauka a nan ya yi Sallolin Magriba da Isha’i a hade (Magriba cikakkiya, Isha’i kasru) ba kuma tare da yin nafila ba. Ana so da an kammala a samu wuri a huta kawai, kamar yadda aka ga Manzon Allah (SAW) ya yi.

Kwanan Muzdalifa na daga cikin sunna, amma an yi sauki ga marasa lafiya ko tsofaffi tukuf-tukuf ko mata masu kiba sosai da ake ji musu tausayin ba za su iya shiga jama’a ba masu yawa, duk sai su yi gaba don su yi Jifa da wuri kana su tafi Makka. Amma matukar mutum lafiyarsa kalau; kar ya yi gaggawa, ya tsaya ya kwana a nan Muzdalifa.

Hadisin ya kuma koyar da mu cewa sunna ce bayan mutum ya kwana a Muzdalifa bayan ya yi Sallar Asuba sai ya kama hanyar Minna zuwa Masallacin Mash’aril Haram ya dan jira zuwa wayewar gari sannan ya nufi wurin Jifa.

Idan mutum ya zo wurin da ake kira Badanil Muhassar sai ya dan yi sauri don a wannan wurin ne Allah ya halakar da Aburahata sa’ilin da ya zo zai rushe Ka’aba. Amma idan mutum bai san wurin ba shi kenan, dama shi wurin Jifa ya nufa.

A wannan ranar, Jifa daya za a yi na Jamratul Akaba da tsakuwa bakwai (wannan Hadisin ya nuna girman tsakuwar kamar na wake ko gyada wadda ko an samu wani ba za a ji ma sa ciwo ba). Duk lokacin da mutum ya daga hannu zai yi Jifar ya ce Allahu Akbar har ya kammala guda bakwan.

Yana daga falalar Jifar shaidan, Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya yi Jifa bai ji (a ransa) cewa an yafe masa zunubansa ba, to a sannan ne ma ya yi laifi.”

Daga nan idan mutum yana Hajjin Kirani ko Tamattu’i ne sai ya nufi wurin da zai yanka dabbarsa, idan ya gama ya yi aski sai ya nufi Makka don yin Dawaful Ifada.

Da zarar ya kammala Dawafin, to komai da aka haramta masa lokacin da ya yi harama ya halasta. Amma idan bai yi wannan Dawafin ba, an halasta ma sa sauran abubuwan da aka haramta wa mai Hajji, sai dai ban da kwanciya da iyali.

Bayan nan sai ya dawo Mina ya yi kwana biyu ko kwana uku. A yayin zaman na Mina kullum mutum zai yi Jifa uku. Daga nan Aikin Hajji ya kare, sai mutum ya je Makka ya yi Dawafin bankwana.

A takaice, wadannan su ne kadan daga cikin darussan Hadisin da Annabi (SAW) ya sanar da cewa duniya ta zo ta ga yadda zai yi Aikin Hajji a shekarar da ya fara yi (SAW).


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Nijeriya Ce Ta 3 A Manyan Kasashe Masu Karfin Masana’antu 10 Na Afirka

Next Post

Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi

Related

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (3)

1 week ago
Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)
Dausayin Musulunci

Yadda Manzon Allah (SAW) Ya Yi Aikin Hajji (1)

3 weeks ago
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci
Dausayin Musulunci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

4 weeks ago
Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Dausayin Musulunci

Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa

1 month ago
Ramadan
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)

2 months ago
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni
Dausayin Musulunci

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

2 months ago
Next Post
Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 – Obi

Cikin Shekaru 2, Tinubu Ya Karɓo Bashi Fiye da Shugabannin Nijeriya 3 - Obi

LABARAI MASU NASABA

Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin

Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin

June 13, 2025
jam'iyyu

Sarkakiyar Da Ke Tattare Da Zaben 2027 Da Yadda Za Ta Kaya

June 13, 2025
Nijeriya Na Kan Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arziki Da Dawo Da Martabar Ƙasa — Ministan Yaɗa Labarai

Nijeriya Na Kan Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arziki Da Dawo Da Martabar Ƙasa — Ministan Yaɗa Labarai

June 13, 2025
Babban Jami’in Diflomasiyyar Kasar Sin Ya Yi Kiran Karfafa Alaka Da Afirka

Babban Jami’in Diflomasiyyar Kasar Sin Ya Yi Kiran Karfafa Alaka Da Afirka

June 13, 2025
Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Gina Kasa A Gabar Da Ake Bikin Cika Shekaru 120 Da Haihuwar Dan Mazan Jiya Chen Yun

Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Gina Kasa A Gabar Da Ake Bikin Cika Shekaru 120 Da Haihuwar Dan Mazan Jiya Chen Yun

June 13, 2025
Pogba Na Shirin Komawa Monaco Bayan Dakatar Da Shi

Pogba Na Shirin Komawa Monaco Bayan Dakatar Da Shi

June 13, 2025
Nijeriya Da Morocco Za Su Sanya Hannu Kan Kulla Yarjejeniyar Aikin Bututun Iskar Gas

Gwamnatin Tarayya Ta Himmatu Wajen Inganta Karfin Sashen Fetur Da Gas Na Cikin Gida

June 13, 2025
Bin Hanya Daya Da Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Muhimmin Mataki Ne Na Ba Da Tabbaci Ga Huldar Ciniki Da Tattalin Arzikin Sin Da Amurka

Bin Hanya Daya Da Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Muhimmin Mataki Ne Na Ba Da Tabbaci Ga Huldar Ciniki Da Tattalin Arzikin Sin Da Amurka

June 13, 2025
Sin Ta Bayyana Adawa Da Keta Hurumin ‘Yanci Tsaro Da Ikon Mulkin Yankunan Iran

Sin Ta Bayyana Adawa Da Keta Hurumin ‘Yanci Tsaro Da Ikon Mulkin Yankunan Iran

June 13, 2025
Gwamnati Ta Yi Karin Haske Kan Biyan Tallafin Rage Radadi Da Mafi Karancin Albashi

Gwamnati Ta Yi Karin Haske Kan Biyan Tallafin Rage Radadi Da Mafi Karancin Albashi

June 13, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.