A cikin watan Oktoba 2024 ne wata tankar Man fetur ta yi hatsarin inda bayan dan lokaci ta kama da wuta a kauyen Majiya da ke karamar hukumar Taura ta Jihar Jigawa.
Hatsarin wanda ya zuwa yanzu, adadin wadanda suka rasu bayan bindigar da tankar ta yi, sun kai 181, tare kuma mutane fiye da 90 da aka kwantar a asibitoci, domin a duba lafiyarsu.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Manjo Janar Olufemi Muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa
Abin nazari a nan shi ne, ba wai kawai aukuwar hatsarin ne abin dubawa ba, amma a zahiri, abin bakin ciki dangane da hatsarin shi ne,yadda yanayin tsarin kasar nan yake, musamman ma na kasa yin wani hobbasan kare rayukan ‘yan Nijeriya marasa karfi a duk lokacin da wani abu irin wannan bala’in ya auku.
Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi, a cikin jimamin sanar da yawan adadin wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin, ya ce, wani dan bangare na hatsarin kawai ya bayyana wasu al’umma saboda munin lamarin.
Sai dai, kuma a bayan aukuwar wannan hatsarin, akwai wasu sauran iyalai da wasu al’ummomi da ke a yankin da hatsarin ya auku ya janyo tarwatsa rayuwarsu.
Har zuwa yanzu dai, tambayar da ake ta famar yi ita ce, shin ta yaya ne, hatsarin ya auku?
Koda yake dai, a martanin da Shugaba kasa Bola Tinubu yayi bayan aukuwar lamarin, ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, gwamnatinsa ta hanyar yin hadaka da gwamnatocin jihohi, za su yi gaggawar daukar matakai a kan aukuwar irin wannan lamarin da kuma yin nazari a kan tsarin yadda ake jigilar man fetur a tankokin man a daukacin kowane sako da lungu na Nijeriya
Kazalika, Tinubu ya umarci hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), da ta kara karfafa matakan yin tafiye-tafiye wadanda suka hada da kara yawan yin sintiri a kan hanyoyin kasar nan, tsaurara bin dokokin yin tuki da saura matakai a kan manyan hanyoyin kasar nan.
Tinubu ya kara da cewa, duk kuma direban da aka samu ya karya su dokokin tukin, duk abinda ya faru da shi, shi ya ja wa kansahi,ya kuma bayar da tabbacin cewar, gwamnatinsa za ta tabbatar da an kiyaye aukuwar irin wadannan hadurran a kasa a nan baki daya.
Sai dai, tambayar mu a nan ita ce, shin wane mataki ne ya dace a dauka akan karuwar asarar yawan rayukan ake za a rika yi kafin Nijeriya ta lalubo da mafita a kan makasudin aukuwar irin wannan annobar ta hatsarin?
Tankar man dai, ta juya ne a babbar hanyar wadda hanyar da ba ta samun kulawar da ta kamata ba.
Wani karin abin takaici anan shi ne, yadda daruruwan mutane a yankin suka fake da kangin talaucin da suke fuskanta, su kai ta yin fitar Farin dango domin zuwa kwasar ganimar man a cikin bokitansu, wanda ba su riga sun farga ba, tartsatsin wuta ya tashi, tankar ta yi bindiga, ta jefa kasar nan a cikin zaman makoki. Aukuwar lamarin dai, bai da wata sarkakiya a cikinsa.
Bugu da kari, bisa rahotannin Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) na 2020 ya nuna cewa, akwai sama da hatsari tankar mai guda 1,500 da suka auku a Nijeriya, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye 535.
A kwana- kwanan nan irin wannan hatsarin ya auku a Jihar Neja, inda mutane 48 suka rasa rayukansa.
Har-ila-yau, har yanzu ana ci gaba da jimamin tashin wutar da ta auku ta kuma lakume ababen hawa a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Ife. Aukuwar wadannan hadduran kawai, sun isa a ce, ba a gamsu da matakan da ake dauka na magance aukuwar lamuran ba a kasa.
Na daya, dogaron da aka yi gaba daya wajen yin jigilar man a hanya domin rabar da man, abu ne da ke da hadarin gaske kuma wanda bai wadatar ba.
Har ila yau, rashin samar da ingancen tsarin safarar kaya a cikin Jirgin kasa a kasar nan, na daga cikin abinda ke janyo ci gaba da asarar rayukan matafiya, bayan alhali, kasashen da suka ci gaba, tuni sun dade suna yin amfani da tsari na zamani, wajen yin jigilar kaya.
Irin wannan annobar da ke faruwa, na da nasaba ne da matsin tattalin arziki da kasar nan ke fama da shi.
Idan aka yi la’akari da yadda wasu talakawan kasar suka sayar da rayuwarsu domn fita kwasar ganimar man, bayan tankokin mai sun fadi, hakan yana nunawa a karara, cewa, talauci ya yiwa wasu al’umomin kasar daurin dema minti.
Bugu da kari, iftibila’in da ya auku na fashewar bututun mai a yankin Jesse a 1998, lamarin ya lakume rayuka sama da 1,000, wanda har yanzu, ana ci gaba da jimamin aukuwar lamarin a kasar.
Kazalika, bayan shekaru sha biyu, sai kuma ace ga irin makamancin i wannnan iftibila’in ya kara aukuwa.
A bisa ra’ayin wannan jaridar, duba da cewa, ra’ayoyin za su iya ban-banta, amma wadannan matsalolin da aka zayyana a sama, har yanzu lamurran ba su sauya ba, musamman kangin talauci, damuwa da kuma karancin kayan aiki.
Har yanzu, ana ci gaba da samun yin bindigar tankokin dakon man wanda kuma sai asarar rayuka, ake kara samu.
Da farko, dole ne mu sauya zuwa yin amfani da tsari na zamani wajen safarar kaya, musamman ma ta hanyar samar da kyakyawan tsarin yin amfani da hanyar Jirgin kasa.
Na biyu kuma, ya zama wajibi a karfafa kiyaye dokokin yin tuki, musamman a lokacin da tankokin mai suka yo dakon man, don kai shi wurin da ya dace su je.
Ya dakyau direbobi a Nijeriya su tabbatar da suna duba lafiyar motocin su dakayu, kafin su fara tunanin fara yin aiki da su.
Sai abu na uku, ya zama wajibi ne mu magance kalubalen da talauci ke jefa ‘yan Nijeriya, wajen daukar irin wadancan matakan.
Bama kamar yadda wasu mutanen suka gwammace su sadaukar da kansu domin zuwa kwasar ‘yar ganimar litocin man, wannan ya nuna yadda mahukunta a kasar, suka kasa samarwa ‘yan kasar kayan biyan bukatunsu yau da kullum.
Iftibla’in da ya auku a Jigawa, abu ne da ya kamata ya zama izina, dangane da jigilar mai ta hanyar yin amfani da hanya, inda kuma a gefe, daya ya nuna cewa, ana fuskantar talauci a kasar Nijeriya.
Wadannan hadurran da suka auku, dama an yi hasashen aukuwarsu, wadanda kuma za a iya dakile aukuwar ta su, wanda hakan ya nuna gazawar mahukunta, wajen kare rayukan ‘yan Nijeria
Idan har ba mu sanya niyyar yin gyara akan lamarin ba, musamman ma ta hanyar samar da sauye-sauye, to tabbas, za a ci gaba da samun asarar rayuka.
Ya kamata ace an inganta rayuwar al’umma, mai makon sai idan wata tankar mai ta fadi ne, za su je kwasar ganima domin biyan bukatun su na yau da kullum ba.