Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana kalaman da gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi a matsayin ‘masu tsauri’, wanda a lokacin da yake yin Allah wadai da kisan mutane 18 da aka yi a yankin karamar hukumarsa a ranar Juma’ar da ta gabata ya ce ba zai taba goyon bayan wani Bafulatani ya sake zama shugaban kasar Najeriya.
Ortom ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar bakuncin takwarorinsa na jihohin Rivers, Oyo, Abia da Enugu a wani liyafar cin abinci a Makurdi, ya ce: “Kuna so in zama bawa ga Bafulatani. Gara in mutu. Ana kashe mutanena kuna so in yi shiru. Ba zan taba goyon bayan Bafulatani ya zama shugaban kasa ba. Idan kuma akwai wani wanda yake shirye ya yi aiki tare da ni don tabbatar da tsaron jama’ata, zan yi aiki da shi.”
Sai dai kungiyar dattawan Arewa a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai da fa’ida, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ta ce kalaman Gwamnan kwata-kwata bai dace da shugaba ba, musamman a daidai lokacin da ake siyasantar da matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Kungiyar ta ce, “mu ma kamar sauran ‘yan Najeriya, mun kalli bidiyon da Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom ke magana a cikin yanayi da kuma yare da bai dace da shugaba ba.
“Kungiyar Dattawan Arewa ta ci gaba da yin Allah-wadai da yanayin kawanya da rashin tsaro da ‘yan Nijeriya suka yi rayuwa a ƙarƙashinsu a cikin ‘yan shekarun nan. Musamman a Arewa ‘yan damfara fulani sun yi fice a matsayin masu kisa da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.
“Ya kamata gwamna Ortom ya cika rantsuwar da ya yi da kuma alkawarin da ya yi na yin rayuwa a matsayinsa na shugaban al’ummarsa.
“Ya kamata ya guje wa sha’awar buga wasan kwaikwayo wanda, kamar sauran ‘yan Najeriya, ke da burin samun sauki da kuma kawo karshen kashe-kashen da ke tayar da juna da kuma kai su ga rikice-rikice marasa iyaka.”