Majalisar dattawan jam’iyyar PDP sun gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, a gidansa da ke Fatakwal, babban birnin jihar.
Wadanda suka halarci taron na sirri, wanda ya dauki sama da sa’o’i biyu, sun hada da sabon zababben shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Philip Tanimu Aduda da kuma Sanata Chukwuka Utazi.
- Zaben Fidda Gwani Na PDP: Wike Shi Ne Wanda Ya Yi Nasara —Orji Kalu
- Gwamnan Bauchi Da Orbih Sun Gana Da Gwamna Wike A Jihar Ribas
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Shuaibu Lau, Sanata Danjuma La’ah da Sanata Barry Mpigi.
Talla
Sai dai babu daya daga cikin wadanda suka halarci taron da ya shaida wa manema labarai abin da ya faru a taron.
Talla