• English
  • Business News
Thursday, October 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Daukakar Nasaba Da Girman Garinsa (SAW)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
12 months ago
Nasaba

Suna daga cikin abin da ba a bukatar a kafa dalili a kansu, in dai kai musulmi ne ba ka bukatar sai an gaya maka daukakar danginsa da girman garinsa da girman inda ya taso, ko ka ce akwai wani bayani mai rikitarwa da sai an maka bayaninsu, ko akwai wani abu boyayye a ciki, shi Annabi (SAW) zababben Bani Hashim ne, ta bangaren kyau, iya magana, Ilimi da dukkan alheri, haka aka san ‘ya’yan Hashimu da wadannan kyawawan halitta.

Ya ishe mu alfahari cewa duk kyawun Abdulmuddalibi, shi ne shugaban Bani Hashim amma gashi yana wa Annabi waka yana cewa “Wa Ab’yadu yustaskal gamamu bi wajhihi, simalul yatama ismatun lil aramili – fari ne wanda da albarkar fuskarsa ake shayar da girgije, Uban marasa Uba kuma mijin mata gwagware.

  • Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Fasaha Da Balagar Harshen Manzon Allah (SAW) II

“Takdi bihin nakatul ajma’u mu’utajiran bil burdikal badri jalla lailataz zulami – rakumi yanayin taku daidai da shi, ya lulluba da bargo kai ka ce wata ne da ya bayyana a cikin dare mai duhu.

“Yaluzu bihil hullaku min ali Hashimin, wahum indahum fi ni’imatin wa fawadili – Halakakkun Bani Hashim da shi suke fakewa, kuma shi (Annabi SAW) mai ni’ima ne da babbar daraja a wajensu”

Shi ne zababben Bani Hashim, haifaffen Bani Hashim, shi ne mafi daukakan Larabawa kuma mafi buwayarsu ta dukkan bangare na Mahaifinsa da bangaren mahaifiyarsa duk babu kamarsa sannan kuma dan garin Makkah ne wacce ita ce mafi girman garuruwan Allah da wajen bayin Allah.

LABARAI MASU NASABA

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

Alkalin Alkalai ya yi mana Hadisi, Hussaini bin Muhammadus Sadafiyyu (Allah Ya rahamshe shi) ya ruwaito Hadisi inda ya daga Salsalar hadisin har zuwa Abu Hurairata daga Annabi (SAW) ya ce: “Bu’istu min kairi kuruni bani Adama, karnan fa karnan, hatta kuntu minal karnillazi kuntu fihi – An tashe ni daga fiyayyen zamaninnikan ‘yan Adam, tsara bayan tsara, tun daga zamanin Annabi Adam har na zo cikin wannan zamanin da nake ciki”

An karba daga Abbas bin Abdulmuddalibi ya ce, Annabi (SAW) ya ce “ Innallaha Ta’ala khalakal khalka waja’alani min kairim, min kairi karnihim, summa takhayyaral kaba’ila, faja’alani min khairi kabilihim, summa takhayyaral buyuta, faja’alani min khairi buyutihim, wa’ana khairihim nafsan wa khairuhum baitan – Lallai Allah Ubanagiji Ya halicci halitta sai ya sanya ni mafificinsu, a cikin mafificin tsaransu, sannan ya zabi kabilu, sai ya sanya ni cikin fiyayyar kabila, Sannan Allah Ya zabi Gida, sai ya sanya ni mafi girman gidansu, ni ne mafi girman ‘yan Adam a kan kaina kuma ni ne mafi girmansu gida.“

An karbo daga Wasila dan Asda’i ya ce, Annabi (SAW) Ya ce “ innallahasdafa min waladi Ibrahim Isma’ila, wasdafa min waladi Isma’ila Bani Kinana, wasdafa min Bani Kinanata Kuraishan, wasdafa min Kuraishan Bani Hashim, wasdafani min Bani Hashim – Allah Ya zabi Annabi Ismail daga cikin ‘ya’yan Annabi Ibrahim (AS), Allah Ya zabi Bani Kinana daga cikin ‘ya’yan Annabi Isma’il, Allah ya zabi Kuraishawa daga cikin Bani Kinana, Allah ya zabi Bani Hashimu daga cikin Kuraishawa, sai Allah Ya zabe ni daga cikin Bani Hashim.”

An karbo daga Abdullahi dan Umar (RA) ya ce, Annabi (SAW) ya ce “Allah Ubangiji madaukaki, ya yi zabe a cikin halittunsa, sai ya zabi ‘ya’yan Adam, a cikin ‘yan Adam sai ya zabi Larabawa, a cikin Larabawa, sai ya zabi Kuraishawa, a cikin Kuraishawa sai Ya zabi Bani Hashimu, a cikin Bani Hashim sai ya zabe ni, ban gushe ba ina abin zabi daga cikin zababbu. Kowa ya sani! duk wanda ya so Larabawa, don yana so na ne yaso su, duk wanda ya ki Larabawa, don yana ki na ne ya ki su.

An karba daga Abdullahi dan Abbas yana cewa ”Ruhin Annabi ta kasance haske ce tana gaban Allah tun kafin ya halicci Annabi Adam da Shekaru 2000 (na kirgen Ubangiji), wannan hasken bai gushe ba yana Tasbihi, Mala’iku ma suna Tasbihi da Tasbihinsa, yayin da Allah Ya Halicci Annabi Adam, sai Allah ya sanya wannan Hasken a tsatson Adamu, sai Allah ya saukar da ni kasa a tsatson Adamu (AS), ya sanya ni a tsatson Annabi Nuhu (AS), ya jefa ni a tsatson Annabi Ibrahim (AS), sannan Allah bai gusheba yana ciro ni daga tsatson masu girma (Maza) da mahaifa (Mata) har ya fitar da ni daga Uwata da Ubana, babu wani ko wata da na biyo ta tsatsonta da suka taba zubar da ruwan banza (lalata ko kuma a ce ain masha’a).

‘Yan uwa masu karatu, hakika girman Annabi (SAW) a wurin Allah ba zai misaltu ba, kamar dai yadda muka rika kawowa cikin darussan da muka gabatar a wannan shafi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2)

October 10, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Next Post
Minista Ya Buƙaci Masu Amfani Da Manhajojin Sada Zumunta Su Riƙa Ƙimanta Nijeriya 

Minista Ya Buƙaci Masu Amfani Da Manhajojin Sada Zumunta Su Riƙa Ƙimanta Nijeriya 

LABARAI MASU NASABA

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

Harkokin Ciniki Da Zuba Jari Tsakanin Sin Da Afirka Sun Samu Ci Gaba Mafi Girma a Shekaru 5 Da Suka Gabata

October 23, 2025
Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

Uwargidan Tinubu Ta Ƙaddamar Da Ɗakin Karatu Na E-learning A Zamfara

October 23, 2025
Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya 

Kasar Sin Ta Karyata Rahoto Na Zuki-ta-malle Da Wata Cibiyar Binciken Amurka Ta Fitar Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Yammacin Afirka

October 23, 2025
An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15

An Kammala Taron JKS Inda Aka Amince Da Shawarwari Kan Shirin Ci Gaban Kasar Sin Na Shekaru Biyar-biyar Karo Na 15

October 23, 2025
Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Tinubu Ya Rantsar Da Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 23, 2025
Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

Sanarwar Bayan Taron Jks: Mene Ne Sirrin Kwarin Gwiwar Kasar Sin?

October 23, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Sojoji Sun Kama Fitaccen Ɗan Bindiga Babawo Badoo Da Wasu 37 A Filato 

October 23, 2025
Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna

Yadda DSS Suka Kama Masu Safarar Makamai Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna

October 23, 2025
Gwamna Abba Ya Jaddada Mubaya’arsa Ga Kwankwaso 

Gwamna Abba Ya Jaddada Mubaya’arsa Ga Kwankwaso 

October 23, 2025
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa

Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa

October 23, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.