Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. ‘Yan uwa masu karatu da ke biye da mu a wannan shafi mai albarka ina muku barka da Juma’atu babbar rana. Mako biyu da suka gabata, darasinmu yana magana ne a kan fasaha da balagar harshen Manzon Allah (SAW).
To, a wannan makon za mu dora da darasi a kan hikimomin kalaman Manzon Allah (SAW).
Hakika an tattaro daga kalmominsa (SAW) wanda babu wani kafin shi da ya taba fada na hikimomi a cikin duk kabilun Larabawa da wadanda ba su ba, shi ya fara fadar su. Babu wani daya daga cikin masu Hikima da za a auna shi da Annabi (SAW).
Yana daga cikin Hikimomin da shi ya fara fadarsu:
Hamiyar wadisu – Tanderu sun yi zafi; Annabi (SAW) ya fada wannan a ranar yakin Hunaini, yaki ya yi yaki, Sahabbai ba dama su gudu su bar Addininsu da Annabinsu, ta bangaren Kafirai su ma sun fito da duk rayuwarsu ba dama su gudu su bar iyalansu, kowa babu damar gudu, yaki ya yi yaki, da Annabi (SAW) yaga irin yadda idon kowa ya rufe ana ta gwabza yaki sai ya ce “Hamiyar wadisu – Tanderu sun yi zafi”.
Mata Hatfa Anfihi – Ya mutu dolensa; Ma’ana ya mutu a gida ko mutuwa irin wacce take zuwa ba tare da ana tsammaninta ba, ko a ce ya mutu cikin lafiya. Larabawa a Jahiliyya da farkon Musulunci ba su so su mutu a gida, an fahimci hakan ne a fadin Sayyidina Umar ga Usman bin Maz’unu yayin da yake cewa “Ina ganin girman Usman bin Maz’unu sai da na ga ya mutu ba a wurin yaki ba, sai na ce ashe ma ba wani ba ne, har sai da na ga Annabi (SAW) Ya Mutu a gida sai na fahimci cewa mutuwar gida ba ita ke nuni da ragwanta ba”. Usman bin Maz’unu Bakuraishe ne, Sufi mai yawan Ibada, shi ne wanda da ya mutu Annabi (SAW) ya yi shaida a kabarinsa yana cewa na yi shaida ne sabida in ‘yan gidana sun mutu in bizne su kusa da shi.
La yuldagul Mumin fi Hujrin Marrataini – Ba a sarar Mumini a cikin rami daya sau biyu; Ma’ana shi Mumini mai takatsantsan ne, idan ya shiga wani lamari ya ga abin bai yi kyau ba, ba zai kara shiga ba. In kuma ya kara shiga lamarin ya sake afkuwa to ya zama wawa.
Assa’idu man wu‘iza bigairihi – Mai arziki shi ne wanda ya gargadu da abin da ya samu waninsa; Ma’ana wanda yaga wani abu ya samu dan uwansa na daga bala’i to ya kamata shi ma ya san abin da dan uwansa ya aikata hakan ta faru da shi, shi ma sai ya kiyaye kafin abin shi ma ya zo kansa.
Irin wadannan suna da yawa wanda mai karatu ba zai iya tattare su ba. Abin da mai duba zai riska su ne mamakai cikin abin da ta tattare su kuma hankali ya tattare ta na daga karshenta.
Sahabbansa sun ce da shi (Annabi Muhammad SAW) Ya Rasulullahi ba mu ga wanda ya fi ka fasaha ba, sai Annabi ya ce “Me zai hana in zama na fi kowa fasaha? Da halshena aka saukar da Alkur’ani” Ma’ana Alkur’ani yarena ne. In Bahaushe bai yi Hikima cikin Larabci ba, ba komai duk da cewa Hausawan suna shiga cikin yaren su koya har su fi ‘yan yaren kwarewa. Kusan duk masu Hadisai kyawawa guda shida ba Larabawa ba ne amma sun kware, Larabci yaren duk Musulmi ne.
Alhamdulillah, yanzu duk wannan karatun da ‘yan Nijeriya suke yi na boko, da (a ce) da yarensu ake karantarwa, da yanzu sun fara kirkire-kirkire, amma dole sai sun fara iya yaren kafin su fara neman sanin ilimin Karatun.
Sannan kuma Annabi (SAW) ya sake fada a wani lokaci “Ana afsahul Arabi, baida anni min Kuraishin, wa nasha’atu fi bani Sa’adin – Ni ne mafi fasahar Larabawa, sai dai ni dan Kuraishawa ne, kuma na tashi a cikin Bani Sa’adin” wannan nau’in maganar yana nufin karfafa yabo ta hanyar nau’in zargi.
Kamar misalin yabon wani malami ga Shehu Ibrahim Kaulaha yake cewa “Shehu Ibrahim, mutum ne mai kyauta, sai dai duk yawan abin da ya ba ka sai ya raina shi (wato shi Shehu ne zai rana abin ba wanda aka ba, ba.”
Don sabida kwadayin ‘ya’yansu su koyi fasaha, Larabawan Birni suke bawa Larabawan Kauye ‘ya’yansu su taso a kauye.
Annabi (SAW) sabida Bakuraishe ne kuma ya taso a bani Sa’adu a kauye sai aka tara masa karfin bara’uwar kauye. Yanzu mutumin kauye da ka fada masa Magana, zai dawo maka da wacce ta fi taka, har ka ji mutum yana cewa ko dai dama yana jira na ne in yi masa magana. Suna da karin magana da bakar magana.
Kuma An hada masa da gogewar lafazin birni da adon maganganun ‘yan birni sannan kuma ka hada da cewa Annabin Allah ne wanda madadinsa ke zuwa daga Allah, wanda Dan’adam bai iya kewayewa da iliminsa.
Ummu Ma’abadin ta fada cikin yadda ta siffanta Annabi (SAW) cewa Maganarsa tana da dadi, a rarrabe yake yin magana, ba magana ‘yar kadan wacce ba ta biya bukata ba kuma ba azarbabi ba (surutu, ba tsayawa, ba ma’ana), kai ka ce maganarsa tsakiya ce da aka tsara, don haka aka rubuta maganarsa a matsayin Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya kasance mai gwarjin murya amma mai dadin murya.
Yanzu kuma bari mu juya akalar darasin namu zuwa abin da ya shafi daukakar Danganensa da girman garinsa da wajen tasowarsa mai girma (SAW).