Minisatan wutar lantarki Adebayo Adelabu ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnatin tarayya ta fara neman wasu hanyoyi na samar da wutar lantarki ga al’ummar arewacin Nijeriya domin rage radadin matsalar wutar lantarki da ake fuskanta a yankin na ‘yan kwanakin nan.
Yankin ta shiga matsalar wuta ne sakamakon lalacewar hanyar wuta daga Shiroro zuwa Kaduna.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- Horor Da Kasar Sin Take Tallafawa Ya Inganta Yaki Da Nakiyoyin Da Aka Binne A Somaliya
Minsitan ya yi wannan bayanin ne bayan ganawarsa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ranar Litinin a fadar shugaban kasa, ya ce, “Muna duba yiyuwar samar da wutar daga layin wuta na Ikot Ekpene da kuma tashar wuta da ke Kalaba.
Ya ce rashin wutar ya shafi jihohi 17 ne a arewacin Nijeriya, kuma gwamnatin tarayya ta amince da daga darajar tashar bayar da wuta na Shiroro Kaduna don ta wadatar da yankin da wutar yadda ya kamata.
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Nijeriya (CNG) sun nuna matukar damuwa kan matsalar wutar lantarki da ta gurgunta wasu sassan Arewacin Nijeriya cikin kwanaki biyar da suka gabata.
Wannan mummunar manufa da ba a taba ganin irinta ba ta jefa miliyoyin gidaje cikin duhu, gurgunta harkokin kasuwanci, da kuma tabarbarewar yanayin tattalin arzikin yankin.
Binciken da kungiyar CNG ta gabatr na farko ya yi nuni da cewa wannan katsewar lantarkin ya samo asali ne sakamakon barna a layin wuta na Shiroro na biyu, wanda ke bai wa manyan tashoshin Kaduna da ke rarraba wa wasu jihohin Arewa wuta.
Mun kuma sani cewa an samu kuskure a layin tsawon watanni. Duk da haka, babu wani hobbasa da aka yi na kokarin ganin an yi gyaran da zai iya cetoa a wannan halin da ake ciki a yanzu.
Mun yi takaicin yadda muka ji cewa manyan na’urori biyu da ke kan wannan layin ba su samu cikakkiyar kulawa ba tun farkon da matsalar ta faru domin dawo da wutar lantarki cikin gaggawa.
Bugu da kari kuma, mafita daya ce tilo, layin Jos,da shima kuma yake a lalace, wanda a halin yanzu TCN ta ce tana kokarin gyarawa, amma ba za ta iya samar da mafita mai dorewa ba.
A yanzu dai wannan ba yanayi ne da za a dogara da shi, kuma yana da ban tsoro sosai.
Rashin kakkarfar tasha a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas:
Kasancewar rashin tsari na bayar da isasshiyar wutar lantarki zuwa yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, kungiyar ta CNG, bayan tattaunawa da masana, ta gano cewa, akwai kuma gibin ababen more rayuwa,.
Duk da kafuwar shirin gyare-gyare da fadadawa (TREP), da nufin samar da hanya mai sauki wajen samar da wutar da ya kunshi kasafin kudi na Dala biliyan 1.661, rashin gudanar da aiki ya hana ta ci gaba.
Bugu da kari, an tanadi sama da Dala miliyan 500 da niyyar tallafa wa kashin bayan bayan aikin na Gabas, wanda zai hada muhimman wurare kamar Sakkwato, Kaura Namoda, Katsina, da sauran su, sakamakon rashin adalci, hakan ya kara kawo tsaiko ga hanyoyin sadarwa game da gudanar da aikins.
Bayan da aka lalata layuka guda biyu (SC) mai karfin kB 330 da ke tsakanin Shiroro da Kaduna, wanda da’ira daya ce daga Jos zuwa Kaduna a yanzu ta wadata yankin Arewa maso Yamma baki daya.
Hakazalika, yankin Arewa maso Gabas ya dogara ne da layin guda daya, wato Jos-Gombe mai kB 330, ma’ana dukkan yankunan biyu suna fuskantar babbar matsala wajen samar da wutar lantarki.
Rashin daidaiton raba wutar lantarki
CNG ta lura cewa Arewa, wacce ke da kaso mai tsoka na yawan al’ummar Nijeriya da ayyukan tattalin arzikinta, abin kunya ba ta da amfani ta fuskar samar da wutar lantarki da rarrabawa.
Yankin ya dogara ne da layukan wutar lantarki na kB 330 guda biyu kacal, yayin da Legas kadai ke amfana da layukan wuta guda takwas. Wannan nuna banbanci da raba kawuna na nuna yanayin rashin kulawa da rashin daidaito a cikin zuba jarin samar da wutar lantarki da aka dade ana yi.
Bugu da kari, Raba wutar lantarki na DisCo a yanzu yana da ban tsoro. DisCos da ke aiki a fadin Arewa, ciki har da Jos ma (MW 60), Kaduna kuma mai (50MW), sai Kano (MW 20), da Yola (30 MW), suna samun MW 160 kawai daga cikin MW 4,249 da ake da su.
Akasin haka, DisCos na Eko da Ikeja a Legas a dunkule suna samun kusan MW 1,400, yayin da Ibadan, Benin, Enugu, da Fatakwal kuma ke amfanar kaso mafi tsoka. Wannan rashin daidaituwar rabo ba kawai ya iyakance yiwuwar dakile ci gaban Arewa bane har ma da bayyana rashin kulawa gare ta.
Bukatar aikin gaggawa da nagargattun ayyuka
Wannan katsewar wutar a halin yanzu, cikin sa’o’i 120 da suka gabata, ya kara jefa masana’antunmu da ke kokarin durkushewa, tare da shakku kan harkokin kasuwanci a cikin dogon lokaci. Mutanenmu, wadanda tuni suke kokawa da kalubalen tattalin arziki, ba za su iya ci gaba da daukar nauyin wannan rashin aiki na rashin tsari ba.
Asibitoci ba za su iya ceton rayuka ba, suna barin marasa lafiya su mutu ba tare da sun iya taimakon su ba.
A cewar Farfesa Uwaifo, “Idan kuna son lalata yanki, to ku lalata wutar lantarki. Idan kana son ka rike yanki zuwa ga mafi ingantacciyar rayuwa, za ka iya yin sa ta hanyar samar da wutar lantarki.” Wannan yana nuni da cewa wasu sun kuduri aniyar ruguza yankinmu, su sa mu zama shalkwatar talauci ta duniya, ta hanyar rage rayuwarmu da hana wurarenmu da asibitoci da masana’antu samun wutar lantarki.
Kungiyar ta CNG tana kira ga Gwamnatin Tarayya, Kamfanin sadarwa na Nijeriya (TCN), gwamnonin Arewa, ‘yan majalisa da duk masu ruwa da tsaki da su gaggauta kokarin ganin an dawo da wuta a Arewa. Dole ne a kula da wannan hanyar da aka biyo ba za amince da ita ba.
Kuma muna bukatar a sake duba tsarin raba wutar lantarki a halin yanzu domin tabbatar da samar da wutar lantarki cikin tsari na gaskiya da adalci a dukkan sassan kasar nan. Muna kira ga Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Gwamnatin Tarayya, TCN, da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) da su bayyana dalilin da ya sa aka yi wannan kaso mai tsoka a wasu wurare, bayan Arewa ce ke da mafi yawan tashoshin samar da wutar lantarki a Nijeriya.
Lallai za a iya fahimtar cewa an bar Arewa da dan karamin kaso na ikon kasa musamman idan aka yi la’akari da muhimmiyar rawar da yankin ke takawa wajen samar da wutar lantarki a kasar nan.
Kiran gaggawa don zuba jari na wutar lantarki ta Arewa
CNG ta yi kira da a kara saka hannun jari a ayyukan samar da wutar lantarki a Arewacin Nijeriya, musamman wajen rabawa. Halin da ake ciki a zahiri ya nuna cewa an bar Arewa a baya da dadewa, rashin isassshiyar wutar lantarki da za ta iya biyan bukatun al’ummarta da tattalin arzikinta. Ba za mu yi kasa a gwiwa a ci gaba da mayar da yankin saniyar ware.
Ku tuna cewa a 2022 CNG ta caccaki mataimakin shugaban kasa na wancan lokacin Yemi Osinbajo kan kudirin sayar da wasu tashoshin samar da wutar lantarki da kamfanin Neja Delta Power Holding Company Limited (NDPHC) ke rike da shi a kasar. A halin da ake ciki kuma, kudaden da aka yi amfani da su wajen samar da wutar lantarkin sun hada da gudunmawar da dukkan jahohi da kananan hukumomi daga Arewa suka bayar tare da yarjejeniyar irin wannan ci gaban kamfanonin samar da wutar lantarki a Arewa.
CNG ta tunatar da gwamnonin Arewa cewa lokaci ya yi da za su nemi kason su daga irin wannan jarin don samun albarkatun da ake bukata don gina ayyukan wutar lantarki masu zaman kansu a jihohinsu; idan ba haka ba, dole ne su matsawa gwamnatin tarayya lamba don ta tattara kayan aiki daga asusunta da na sauran jihohi don kafa wasu tashoshin wutar lantarki kamar yadda ta yi da masana’antar da aka kafa a Kudu.
Kungiyar ta CNG wadda ta sha kalubalantar Gwamnati kan gazawarta wajen mutunta yarjejeniyar samar da kayayyakin more rayuwa iri daya a yankin Arewa, an tabbatar da sakamakon da ya fara bayyana a halin yanzu gabaki daya wanda zai ci gaba da addabar Arewacin Nijeriya baki daya, ta dakile yunkurin ci gabanta na tsawon shekaru masu zuwa sai dai idan ba a yi magance matsalar kai tsaye ba.
Don haka, CNG a matsayin ba wa Arewa fifiko, ta bukaci gwamnonin Arewa, Sanatoci, ’yan Majalisar Wakilai da su yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su yi aiki tare, su kuma bukaci a zuba jari mai kyau a kan kamfanonin samar da wutar lantarki a Arewa, saboda an yi amfani da albarkatunsu wajen bunkasa wutar lantarki. a Kudu.
Lokaci ya yi da za a dauki mataki mai tsauri. Muna kira ga gwamnati da ta dawo da wutar lantarki nan take, tare da bai wa Arewa fifiko wajen ayyukan samar da wutar lantarki da tsare-tsare na samar da ababen more rayuwa.
Duk wani abu da za a kwange zai zama cin amana ga hakkin yankin na samun ci gaba na gaskiya da adalci a rabon albarkatun wutar lantarki na kasa, wanda ba za a amince da shi ba.
Kungiyar ta CNG tana tunatar da gwamnatocin jihohi da ‘yan majalisa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa daga yankin Arewa bukatar tunkarar wannan al’amari ga Shugaban kasa kai tsaye da kuma baki daya a matsayin wani lamari na gaggawa mai dauke da damuwa.