An naɗa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yayin da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya zama sakataren riƙon ƙwarya na jam’iyyar.
Aregbesola ya amince da wannan muƙami ne cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa shugabanni da mambobin jam’iyyar ADC a ranar Talata.
- Rikicin Gonar Gado Ya Yi Ajalin Mutum Ɗaya, An Ƙone Gidaje A Filato
- An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa
A cikin wasiƙar, Aregbesola ya ce ya karɓi wannan matsayi da niyyar yin hidima ga al’umma, ƙasa, da jam’iyyar.
Ya gode wa shugabancin jam’iyyar bisa amincewar da suka yi da shi, tare da yaba wa mambobin jam’iyyar da ke da yaƙinin cewa siyasa ya kamata ta zama alheri ga jama’a.
Ya ce jam’iyyar siyasa ba kawai don lashe zaɓe ake buƙatarta ba, don taimaka wa jama’a da inganta rayuwarsu.
Aregbesola, wanda shi ne tsohon Gwamnan Jihar Osun, ya ƙara da cewa jam’iyyar siyasa bai kamata ta zama hanyar neman mulki kawai ba ko wata dama ga wasu tsiraru ba.
Ya ce jam’iyya ta gaskiya ita ce wadda ke da tsari da manufa, kuma wadda ke aiki don jama’ar da ta ke wakilta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp