• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dawowar Ta’asar Boko Haram: An Kashe Maciji Ba A Sare Kan Ba – Mazauna Gabas

byMuhammad Maitela
2 years ago
boko haram

Jama’a sun fara bayyana shakku dangane da yadda a ‘yan kwanakin nan ake fuskantar barazanar dawowar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a jihohin Borno da Yobe, a daidai lokacin da ake tsammanin an raka bako; ashe yana labe a bayan gari.

Hakan ya biyo bayan wasu munanan hare-haren da mayakan ke ci gaba da aiwatar wa a wasu sassan jihohin biyu, wadanda suka dade suna fada da rikicin wanda ya jawo asarar dimbin rayukan al’umma tare da barnata dukiya ta biliyoyin naira; baya ga raunata dubban jama’a.

  • Zulum Ya Daukaka Darajar Kwalejin Larabci Zuwa Babbar Cibiyar Yaki Da Akidun Boko Haram
  • ISWAP Ta Hallaka Kwamandan Boko Haram A Sambisa

Cikin kasa ga wata daya, mayakan sun aiwatar da munanan hare-haren da suka jawo salwantar rayuka sama da 50, wanda a makon da ya gabata, mayakan sun kashe kimanin mutum 40 a kauyen Nguro-kayya dake karamar hukumar Gaidam a jihar Yobe, baya ga halaka wani jami’in hukumar hana fasa kauri ta Nijeriya a garin na Gaidam.

Yayin da a cikin wannan makon, mayakan na Boko Haram sun halaka manoman shinkafa 13, a cikin wani sabon harin d suka kai a kauyukan Karkut da Koshebe dake cikin karamar hukumar Mafa a jihar Borno.

LEADERSHIP Hausa ta zanta da wani magidanci daga garin Gaidam (bai aminta a bayyana sunan sa ba) a jihar Yobe, ya ce: “Zancen a ce babu Boko Haram bai taso ba, saboda kusan kana fita daga garin Gaidam kadan; ta bangaren gabas da Arewaci, za ka ci karo da yan Boko Haram, wanda tun a wancan lokacin su suke karbar haraji a hannun mazauna kauyuka.”

LABARAI MASU NASABA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

“Gaskiyar magana ita ce, har yanzu akwai sauran rina a kaba, saboda har yanzu yaran nan (Boko Haram) suna nan a kauyuka, ba sa jin tsoro ko shakkar wani mutum. Suna nan a cikin tsaunuka da dazuka tare da wasu kauyuka.”

“Kuma abin da ya sa ba a jin diriyarsu a lokacin damina shi ne gittawar ruwan Kogin Kumadugu, amma da zaran ya yanke za kana ganin su. Musamman tun daga gabashin Gaidam har zuwa Tafkin Chadi, wanda ana iya cewa sun mayar da yankin tamkar daularsu. Babu abin da mutum zai yi har sai da izinin su tare da biyan haraji.” Ya bayyana.

Shi ma wani bawan Allah da wakilinmu ya tattauna da shi ta wayar tafi da gidanka (bai yarda na bayyana sunan shi ba, saboda yanayin tsaro) a Yadin-Buni dake jihar Yobe, ya bayyana cewa, “ba zan ce ba a gama da Boko Haram ba, to amma gaskiyar magana shi ne an kashe maciji ba a sare kansa ba. Saboda har yanzu akwai yankunan da ba ma shiga a nan.”

“Idan ba ka manta ba, a kwanan baya ma sun yi wa wasu matasanmu sama da 10 kwanton-bauna, inda suka halaka su har lahira. Sannan har yanzun nan da nake magana da kai, kowane lokaci a cikin fargaba al’ummar kauyukanmu suke; saboda kowane lokaci zaman dar-dar ake.” In ji shi.

Jama’a da dama a wadannan jihohin suna ci gaba da bayyana ra’ayoyi daban-daban dangane da sabbin hare-haren tare da bayyana cewa ya kamata gwamnati ta sake nazarin matakan da ta bi wajen karbar tuban wasu daga cikin mayakan Boko Haram da ta yi a baya, inda ra’ayoyin ke nuni da cewa sai da dan gari a kan ci gari.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya
Labarai

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba
Labarai

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci
Labarai

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Next Post
ASUU

Cire Kashi 40 Na Kudin Shigar Jami’o’i Zai Kassara Su - ASUU

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version